Tsohon janar a rundunar soji ya kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

Tsohon janar a rundunar soji ya kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

- Tsohon shugaban hafsoshin Najeriya, Janar Ipoola Alani Akinrinade ya yiwa 'yan Najeriya karatun ta natsu a kan daukar shawarar tsohon shugaban kasa Obasanjo

- Janar Akinrinade ya ce Obasanjo ya yi kaurin suna a matsayin mutum mara hangen nesa da kaifin basira a lokacin da ya ke kwandan soji a lokacin yakin basasar Najeriya

- Tsohon Janar din ya ce Obasanjo ya dade yana yaudarar 'yan Najeriya ta hanyar fada musu wanda za su zaba kuma lokaci ya yi da ya kamata ayi watsi da shi

Tsohon shugaban hafsin sojojin Najeriya kuma jagoran kungiyar Afenifere, Janar Alani Akinrinade ya ce marawa Atiku Abubakar baya a matsayin dan takarar shugabancin kasa da Obasanjo ya yi 'rainin hankali ne ga 'yan Najeriya.

Akinrinade ya bayyana takaicinsa a kan zabin na Obasanjo a shafin jaridar Punch na ranar Alhamis inda ya shawarci 'yan Najeriya suyi watsi da Obasanjo da dukkan shawarwarinsa.

Wani Janar din soja ya kwancewa Obasanjo zani a kasuwa
Wani Janar din soja ya kwancewa Obasanjo zani a kasuwa
Asali: Twitter

Jagoran na Afenifere ya bayar da misalan rashin tunani da kaifin basira na Obasanjo a lokacin da ya ke kwamandan rundunar soji a yakin basasar Najeriya. Ya yi ikirarin cewar rashin hangen nesa na Obasanjo ya yi sanadiyar mutuwar dubban sojoji a filin daga.

DUBA WANNAN: Kamfen: Taron Atiku a jihar Borno ya bayar da mamamki, hotuna

"Ina yiwa 'yan Najeriya gargadi kada su bi shawarar Obasanjo a wannan karon saboda ya aikata hakan a baya. Shin har sau nawa za mu bari Obasanjo ya yaudari 'yan Najeriya?

"Wasu daga cikin mu da muka san shi a aikin soja mun san cewa Obasanjo ba shi da hikima da hangen nesa.

"Najeriya tayi asarar dubban sojoji saboda rashin hikima da hangen nesa na Obasanjo a filin daga. Ba don rashin makamai da abincin ba, da 'yan Biafra sun ci galaba a kan sojojin Najeriya. Alabi Isama ya yi sahihiyar bayani a kan wannan lamarin a litafinsa mai suna 'The Tragedy of Victory' saboda haka babu bukatar mu maimaita kuskuren.

"Idan ka duba tarihi za ka ga yadda Obasanjo ya yi shige da fice har Shehu Shagari ya zama shugabab kasa a madadin Obafemi Awolowo da ya fi shi gogewa. Bayan mulkinsa karo na biyu, ya kakabawa 'yan Najeriya Umaru 'Yar'adua duk da yasan bashi da lafiya tare da mataimakinsa Goodluck Jonathan. Ya hana dukkan sauran masu sha'awar takarar su kai labarai ta hanyar barazana da bita da kulli."

"A 2015 shi kuma ya ce 'yan Najeriya su zabi Buhari kamar yadda ya marawa sauran 'yan takarar shugabancin kasa da suka gabaci shi yanzu kuma ya ce Buhari ya gaza. Bayan ya gama kushe Atiku Abubakar yanzu kuma ya sake dawowa ya ce mu zabi Atikun."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel