PDPn Tambawal na can yana saye quri'un Sokoto - APC ga INEC

PDPn Tambawal na can yana saye quri'un Sokoto - APC ga INEC

- Tambawal ya koma PDP da niyyar takarar shugaban kasa a bara

- Atiku ya tika shi da kasa amma yace za'ayi aiki tare

- Wasu na ganin sai dai da sayen Quri'u zai iya kawo jihar, tunda Wamakko bai bishi ba

PDPn Tambawal na can yana saye quri'un Sokoto - APC ga INEC

PDPn Tambawal na can yana saye quri'un Sokoto - APC ga INEC
Source: Twitter

APC Sokoto, ta rattaba wa INEC da hukumomin tsaro, kan wai yadda ake ta bin talakawa ana damqa musu kudi a amshe katunan zaben su, domin zabukan gwamna da ma na shugaban kasa.

A gefe guda kuma, tayi kira ga jama'a dasu yi wa kansu kiyamul layli su bar sayar da katunan su ga 'yan siyasa, wadanda ke son su kwace musu gobensu.

A Sokoto dai a watan fabrairu akwai kallo, tunda Tambawal ya bar Ogansa Wamakko ya koma PDP, ya kuma kawo Atiku a matsayin wanda yake so su zaba.

GA WANNAN: Cin hanci ya karu a Amurka, bayan da ya sauka a Najeriya, a sabon rahoton masu sanya idanu

An dai zubar da dala da sunan Amuni Tambawal a birnin Fatakwal, inda Nyesom Wike yaso lallai PDP ta tsayar dashi domin watakil ya samu yayi mataimaki ga Tambawal din.

Sakataren yada labarai na jam'iyyar APCn, Sambo Bello Danchadi dai shine yayi wannan zargi, inda yace wasu mata ne ke shiga gidajen mutane, su amshe katunan zaben mutane bayan sun basu 'yan kudi, ko dai don suyi amffani dasu ko don su lalata su, tunda wai a cewarsa, jama'ar Sokoto Buhari zata zaba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel