Aiki na kyau: Sojoji sun halaka yan bindiga 21, sun ceto mutane 89 da aka yi garkuwa dasu

Aiki na kyau: Sojoji sun halaka yan bindiga 21, sun ceto mutane 89 da aka yi garkuwa dasu

Dakarun rundunar Sojoji ta Operation sharan daji dake aikin tabbatar da tsaro a tsakanin jihohon Katsina, Zamfara da Sakkwato sun halaka yan bindiga guda 21 a wani muhimmin samame da suka kai a sansanoninsu, sa’annan suka ceto mutane 89 dake hannunsu.

Mukaddashin kaakakin rundunar, Manjo Clement Abiade ne ya sanar da haka a ranar Talata 29 ga watan Janairu na shekarar 2019, inda yace Sojojin sun samu wannan nasara ce cikin sati daya kacal, inda suka kashe yan bindiga 21, suka kama wasu 17 da ransu.

KU KARANTA: Sallamar Onnoghen: Atiku ya kai korafin Buhari gaban manyan kasashen duniya akan laifuka 5

Haka zalika majiyar Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana cewa an samu asarar rayuka daga bangaren fararen hula, inda aka kashe mutane goma sha daya, da kuma wani Sojan sa kai na Civilian JTF guda daya.

Sanarwar ta kara da cewa Sojoji sun samu nasarar fatattakar yan bindigan da wasu sansanoni da suke amfani dasu a matsayin mabuya tare da kaddamar da hare hare daga cikinsu, sa’annan suka banka musu wuta gabaki daya, bayan sun ceto mutane 89 da suke rike a sansanonin.

Bugu da kari, Manjo Clement yace sun kama wasu mutane biyu, Musa Amadu da Auwalu Muntari dukkaninsu mazauna kauyen Danfumi, wadanda yace suna kai ma yan bindigan bayanan sirri, kuma a yanzu haka suna taimaka ma Sojoji da bayanai.

Kaakakin ya lissafa garuruwan da suka yi arangama da bindiga da suka hada da Shinkafi, Birnin Magaji, Maru a jahar Zamfara, sai kuma Safana, Runka, Kukan Sama a jahar Katsina, inda yace sun kwato makamai da suka hada da bindiga mai baki biyu, kananan bindigu 2, alburusai, babura 4 da kwayoyi.

Daga karshe kaakakin ya isar da sakon ta’aziyyar babban kwamandan Operation sharan daji ga iyalai da yan uwan sojan sa kai na civilian JTF da ya mutu a yayin musayar wuta da yan bindigan, sa’annan ya bada tabbacin zasu cigaba da aiki tukuru don ganin sun kakkabe yan bindiga daga jihohin gaba daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel