Malaman Makaranta sun yiwa Buhari bugun kalangun nasara a jihar Katsina

Malaman Makaranta sun yiwa Buhari bugun kalangun nasara a jihar Katsina

- Malamai sun yi dandazon bayyana goyon bayan kudirin tazarcen shugaba Buhari da kuma Gwamna Masari a jihar Katsina

- Gwamna Masari ya yabawa goyon bayan Malamai tare da jinjina kasancewar su tubali kuma ginshikin ci gaban kowace al'umma

- An nemi Malamai da su tabbatar da nasarar shugaba Buhari da kuma gwamna Masari domin ci gaba da kwankwadar romo na jin dadi

Mun samu cewa cikin tarayya da juna, malaman makarantun firamare da sakandire sun yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari bugu irin na kalangun nasarar tazarce yayin wani dandazo da suka gudanar yau Talata a birnin Katsinan Dikko.

Malaman da suka fito daga cikin dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Kastin sun hallara a harabar filin wasanni ta Muhammadu Dikko mai lakabin Karakanda domin nuna goyon bayan su tukuru ga shugaban kasa Buhari da kuma gwamnan jihar, Aminu Bello Masari.

Yayin taron da kimanin malamai kimanin 3000 suka gudanar na goyon bayan kudirin tazarcen shugaba Buhari da kuma gwamnan jihar Katsina, Masari ya yabawa wannan goyon baya na malamai da cewar sa sun kasance tubali na ci gaban kowace al'umma.

Shugaban kasa Buhari bayan halartar sallar idi a garin Daura na jihar Katsina
Shugaban kasa Buhari bayan halartar sallar idi a garin Daura na jihar Katsina
Asali: Facebook

Cikin annashuwa da farin ciki, gwamna Masari ya ce muhimmiyar rawar da Malamai ke takawa ba ta iyaka ballantana misali, da ya ce hakan ya sanya gwamnatin sa ta bai wa fannin ilimi muhimmancin gaske tun yayin karbar ragamar jagoranci.

Ya ke cewa, dole Malamai su mike tsaye wurjajan wajen kafa tubali da tanadar ginshiki na samar da nagartattun manyan gobe da ke da tasirin gaske wajen tabbatar da kyakkyawar makoma ga kasa baki daya.

KARANTA KUMA: Obasanjo da Buhari sun sadu cikin raha a fadar shugaban kasa

A nasa jawaban, kwamishinan ilimi na jihar, Dakta Badamasi Lawal, ya ce an samu kyakkyawan sauyi a fannin da kuma ma'aikatar ilimi ta jihar kama daga inganta ci gaban gine-gine, biyan albashi akan kari da kuma inganta jin dadin malamai.

Ya yi kira ga Malaman da su ramawa Kura kyakkyawar aniyyar ta wajen goyon baya tare da tabbatar da dawowar shugaban kasa Buhari da kuma gwamna Masari bisa kujerar mulki a zaben bana domin ci gaba da sharbar romo na jin dadi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng