Rundunar Sojan sama ta tura dakarunta da jiragen yaki zuwa Sakkwato

Rundunar Sojan sama ta tura dakarunta da jiragen yaki zuwa Sakkwato

Rundunar Sojan samar Najeriya ta tura da dakarunta na musamman zuwa jahar Sakkwato tare da jiragen yaki domin su bankado sansanoni da wuraren da yan bindiga suke fakewa tare da samun mafaka a jahar, kamar yadda rundunar ta bayyana.

Kwamandan dabarun yakin sama, Iya mashal Isiaka Oladayo Amao ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 20 ga watan Feburairu, a filin sauka da tashin jirage na Sultan Abubakar dake garin Sakkwato, inda yace manufar tura Sojojin shine tabbatar da tsaro a jahar.

KU KARANTA: Jerin jam’iyyun Najeriya 13 da suka tsayar da Buhari a matsayin dan takararsu

Rundunar Sojan sama ta tura dakarunta da jiragen yaji zuwa Sakkwato
Sojoji
Asali: UGC

“Mun turaku Sakkwato ne domin cika alkawarin da babban hafsan Sojan sama ya dauka ne a shekarar data gabata, a yayin wata ziyara daya kai jahar a shekarar data gabata, yayin da ya fahimci akwai matsala a sha’anin tsaro a jahar Sakkwato.

“Matsalar na faruwa ne sakamakon aikin da Sojoji ke yi a dazukan jahar Zamfara inda suke fatattakar yan bindiga, haka ne yasa wasunsu suke hijira zuwa jahar Sakkwato, inda a yanzu haka suka fara kai hare hare zuwa wasu kauyukan jahar.

Rundunar Sojan sama ta tura dakarunta da jiragen yaji zuwa Sakkwato
Sojoji
Asali: Facebook

“Mun kawo nan ne domin ku gudanar da aiki, aikin da zaku yi shine fatattakar yan bindiga daga jahar Sakkwato gaba daya, ta hanyar aiki hannu da hannu da sauran kungiyoyin tsaro dake jahar. Mun sama muku jiragen yaki da zasu taimaka muku aikinku.” Inji shi.

Daga karshe kwamanda Amao yace rundunar za ta yi amfani da filin sauka da tashin jirage na jahar Sakkwato da na jahar Katsina wajen jigilar Sojojin, sa’annan ya basu tabbacin akwai isashshen man jirgi, da sauran kayan aikin da zasu taimaka musu wajen gudanar da wannan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng