Jerin jam’iyyun Najeriya 13 da suka tsayar da Buhari a matsayin dan takararsu

Jerin jam’iyyun Najeriya 13 da suka tsayar da Buhari a matsayin dan takararsu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyan farin cikinsa game da matakin da wasu jerin gwanon jam’iyyun siyasar Najeriya suka dauka na mara amince da takararsa tare da mara masa baya a zaben 2019 dake karatowa.

Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne yayin da ya karbi bakoncin hadaddiyar kungiyar jam’iyyu masu son cigaban Najeriya, CPPP, a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, a ranar Juma’a 18 ga watan Janairu.

KU KARANTA: An fara biyan yan Najeriya makudan kudi domin su fita daga wata kasar Turai

Jerin jam’iyyun Najeriya 13 da suka tsayar da Buhari a matsayin dan takararsu
Buhari da Bashir
Source: Facebook

Kungiyar tace ta kai ma Buhari ziyara ne domin jaddada goyon bayansu gareshi kamar yadda suka yi a zaben 2015, inda Buhari ya bayyana farincikinsa tare da amincewa da bukatarsu, kamar yadda suka nema.

A jawabinsa, Buhari yace: “Na gamsu da dagiyarku, mutuncinku, martabarku da kuma jajircewa, na ji dadin matakin da kuka dauka na goyon bayana a zaben 2019, na yaba da amincewar da kuka nuna mini, kuma wannan ziyara taku ta kara min kwarin gwiwa.” Inji shi.

Shugaban tawagar, Bashir Yusuf Ibrahim ya bayyana cewa matakin da suka dauka na goyon bayan Buhari baya rasa nasaba da kokarin da yayi a fagen shimfida ayyukan alheri ga yan Najeriya, tare da nasarorin da aka samu akan ayyukan.

Bashir yace sun gamsu da ayyukan cigaba da gwamnatin Buhari ke shimfida ma yan Najeriya, musamman yaki da masu garkuwa da mutane, yan bindiga, barayin shanu, yaki da rashawa da kuma yaki da ta’addanci.

Jam’iyyu 13 da suka mara ma Buhari baya sun hada da; Advanced Allied Party-AAP; Africa Peoples Alliance-APA; Freedom & Justice Party-FJP; KOWA Party; New Progressive Movement-NPM; Peoples Democratic Movement-PDM; da Accord Party-AC.

Sauran sun hada da; Sustainable National Party-SNP; New Nigeria Peoples Party-NNPP; Unity Party of Nigeria-UPN; United Progressive Party-UPP; National Democratic Liberty Party-NDLP; Nigeria Elements Progressive Party-NEPP; da Yes Electoral Party-YEP.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel