Ra’ayin Gumi, Dahiru Bauchi, Jingir, Bala Lau da Yusuf Sambo game da zaben Buhari da Atiku

Ra’ayin Gumi, Dahiru Bauchi, Jingir, Bala Lau da Yusuf Sambo game da zaben Buhari da Atiku

A yayin da zaben 2019 na gama gari ke cigaba da karatowa, babu ta yadda za’a raba addini da tasirin Malamai ga siyasa musamman ma a yankin Arewacin Najeriya, yankin da al’ummar Musulmai suka fi yawa.

Za’a fahimci haka idan aka yi duba ga yadda Malaman addinin Musulunci ke tasiri matuka ga ra’ayin mabiyansu musulmai wajen goyon bayan wani dan siyasa a zabukan da suka gabata a shekarun baya, tun daga 1999 zuwa 2015.

KU KARANTA; An karrama mutane 6 da suka nuna halaye irin na Sir Ahmadu Bello Sardauna a Kaduna

Ra’ayin Gumi, Dahiru Bauchi, Jingir, Bala Lau da Yusuf Sambo game da zaben Buhari da Atiku
Malamai
Asali: UGC

Legit.ng ta ruwaito sakamakon yawan malaman dake bayar da fatawa ga mabiyansu da kuma yawan kungiyoyin addinin, don haka ake samun sabanin ra’ayi a tsakanin malaman kansu, wanda hakan ke zamtowa wata kafa da yan siyasa ke amfani da ita wajen raba kawunansu.

A yanzu ma da ake tunkarar babban zaben 2019 ma an fara samun irin wannan banbamce banbamcen ra’ayi game da yan takarar da suka fi dacewa Musulmai su zaba domin su jagoranci al’amuransu a gwamnati.

Sai dai a yanzu an fi samun wannan cece kuce akan takarar kujerar shugaban kasar Najeriya, inda musulmai biyu suka fito takara suna neman yan Najeriya su zabesu, watau shugaban kasa Muhammadu Buhari dake neman tazarce, da Atiku Abubakar dake neman kawar da Buhari.

A baya an jiyo shehin Malamin nan daga jahar Kaduna, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi yana kira ga zaben Atiku Abubakar a kaikaice, amma daga bisani ya sauya ra’ayi, inda yayi kira ga a kyale jama’a su zabi wanda suke so.

Shi kuma shugaban Izala, Sheikh Bala Lau kira yayi ga yan kungiyar Izala dasu zabi shugaba Buhari, yayin da shugaban kungiyar Izalar Jos Sheikh Sani Yahaya Jingir yace ba zai iya zaban Inyamuri a matsayin shugaba ba (Nuni ga mataimakin Atiku, Peter Obi), don haka Buhari zai zaba.

Sai dai ra’ayi ya sha bambam tsakanin Jingir da mataimakinsa Yusuf Sambo Rigachikun, wanda yace shi kam Atiku Abubakar zai zaba, dalilinsa kuwa shine yafi Buhari kishin musulunci, a cewarsa ya gina Masallatai fiye da 100.

Na baya bayan nan da yayi tsokaci game da takarar Atiku da Buhari shine Sheikh Abubakar Gero Argungu, wanda yace duka mabiya Izalar Jos da ta Kaduna shugaba Buhari zasu zaba ba tantama.

Amma fa masana siyasar Najeriya na ganin a yanzu idon mutane ya bude, ba lallai bane malamai su yi tasiri wajen karkatar da ra'ayinsu waje zaben wani dan takara ko waninsa ba, don haka sai dai an tashi, kamar yadda masu kallon kwallo suke cewa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel