Wani Jikan Maulana Inyass ya na neman Gwamnan Jihar Kano a 2019

Wani Jikan Maulana Inyass ya na neman Gwamnan Jihar Kano a 2019

Mun ji labari cewa ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar AGA ta All Grassroots Alliance watau Shehu Tijjani Sani Auwalu Darma, yana da alaka da gidan Sheikh Shehu Ibrahim Inyass.

Wani Jikan Maulana Inyass ya na neman Gwamnan Jihar Kano a 2019
Jikan Shehi Ibrahim Inyassa zai yi takara da Ganduje da Takai
Asali: UGC

‘Dan takara jam’iyyar AGA a Kano jika ne wajen babban Shehin Malami Ibrahim Inyass. wanda aka fi sani da Barhama ko Gausu. Yanzu dai Tijjani Sani Auwalu Darma yana cigaba da kamfe inda yake neman jama’a su zabe sa a 2019.

Shehu Tijjani Darma ya bayyana nasabar sa da gidan Shehi Ibrahim Inyass ne a wajen kaddamar da yakin neman zaben sa a wani dakin taro da ke cikin babban masallacin Shehu Ahmadu Tijjani da ke Unguwar Kofar Mata a cikin Kano.

Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, ‘dan takarar ya nunawa jama’a cewa abin da ake bukata wajen shugabanci shi ne tsoron Allah domin kamanta adalci. Shehu ya kuma bayyana cewa ya janyo Malamai da za su rika ba sa shawara.

KU KARANTA: Za mu ci zabe a Jihar Kano - tsohon Gwamna Kwankwaso

‘Dan takarar ya kuma bayyana cewa zai rika girmama ra’yin jama’a idan ya kafa gwamnatin sa. Alhaji Shehu Sani Darma ya koka da halin da al’umma musamman na cikin karkara su ka shiga a wannan mara inda yayi alkawain kawo masu sa’ida.

Jikan wannan Shehin Malami da aka yi ya fadakar da jama’a cewa duk da cewa yana tare da Mabiya Darikar Tijjaniya a jam’iyyar sa, wannan ba zai sa ya fifita su a kan sauran al’ummar jihar Kano masu mabanbantan dariku da kuma addinai ba

Shehi Ibrahim Inyass dai babban Malami ne a Darikar Tijjaniya wanda ya kuma yi fice musamman a yankin mu na Afrika. Inyass yana ikirarin cewa yana da nasaba da gidan Manzon Allah SAW.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel