Kwankwaso: Shugaba da magoya bayan Kwankwasiyya 200 sun koma APC a Katsina

Kwankwaso: Shugaba da magoya bayan Kwankwasiyya 200 sun koma APC a Katsina

A yayin da zaben shugaban kasa da na gwamnoni ke kara matsowa, shugaban darikar siyasa ta Kwankwasiyya a jihar Katsina, Alhaji Inusa Dankama, ya jagoranci mambobi 200 canja sheka daga PDP zuwa APC.

Kazalika, masu canja shekar sun bayyana janye goyon bayansu ga shugaban darikar Kwankwasiyya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, yayin taron gangamin jam'iyyar APC a karamar hukumar Kaita da aka yi jiya, Litinin.

A jawabinsa a wurin taron, Dankama ya bayyana cewar sun bar Kwankwasiyya da jam'iyyar PDP ne saboda kokarin da gwamnatin APC ta yi a jihar Katsina a bangaren taimakon rayuwar matasa tun bayan fara mulki a shekarar 2015.

Da yake karbar masu canjin shekar, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shaida masu cewar jam'iyyar APC gida ce a wurinsu, sannan ya kara da cewa dama can an yaudare su ne zuwa PDP domin a yi amfani da su wajen biyan bukatar wani mutum.

Kwankwaso: Shugaba da magoya bayan Kwankwasiyya 200 sun koma APC a Katsina
Kwankwaso a wurin taron Kwankwasiyya
Asali: Twitter

A wani labarin na Legit.ng daga Katsina, kun ji cewar rundunar 'yan sanda reshen jihar ta sanar da samun nasarar kama wasu mutane biyu da suka garkuwa da wata dattijuwa a karamar hukumar Safana.

A wani jawabi da ya yi ga manema labarai a hedkwatar 'yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce sun kama 'yan ta'addar biyu ne bayan samun bayanan sirri.

Ya ce masu garkuwa da mutanen sun amsa laifinsu, kuma matar da suka yi garkuwa da ita ta tabbatar da cewar sune suka sace ta.

DUBA WANNAN: Tashin hankali: 'Yan bindiga sun hallaka mutane 26 a Sokoto

Kazalika, Isah ya ce sun yi nasarar kama wani dan fashi tare da kwace wata mota kirar Toyota Highlander da ya yi fashinta.

"A ranar 7 ga watan Janairu jami'an 'yan sanda suka yi nasarar kama wani matashi, Mohammed Sani, mai shekaru 28 dan asalin karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa da wata motar sata yayin da yake kokarin tsallaka wa zuwa janhuriyar Nijar," a cewar Isah.

Kakakin ya ce motar kirar Toyota Highlander mai launin tasa, na dauke da lambar mallaka kamar haka; ABC 572 RN da kuma lambar kira JTEEP21A560186921.

Isah ya kara da cewa matashin ya amsa laifinsa tare da shaida wa rundunar 'yan sanda cewar ya yi fashin motar ne a garin Jos, jihar Filato.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel