Fasaha: An fara koyawa matasa a arewa gini da roba
Wata kungiya mai zaman kanta (DARE) ta fara bawa matasan Kaduna horo a kan sabuwar fasahar amfani da sarrafa bola, musamman domin amfani a gine-gine.
Sabuwar fasahar zata bawa matasan damar koyon sarrafa bola domin yin rufi a gidaje, mayar da ita intalok, da kuma yiwa gidaje kwalliya.
Shugaban kungiyar, Mista Yahaya Ahmed, ne ya sanar da hakan ga manema labarai yayin wata hira da shi a garin Kaduna, wacce aka yi ranar Lahadi, 6 ga watan Janairu, 2019.
Ahmed, mai ilimin Injiniya, ya ce fasahar irinta ce ta farko a Najeriya da wasu sassan Afrika.
"Wannnan fasaha ce da an gwada kuma an tabbatar da ita. Fasaha ce da zata taimaka wajen tsaftace muhalli da kuma inganta tattalin arzikin jama'a da kasa baki daya.
"Da wannan fasaha jama'a zasu samu damar mallakar muhalli mai kyau cikin farashi mai sauki, domin bola bata da tsada.
"Mun dade muna aiki a kan wannan fasaha bayan mun yi nazari a kanta.
"Yanzu haka muna magana da abokan mu dake kasar Ingila da Jamus, domin wannan fasaha daga wata hukumar sarrafa bola a kasar Ingila ta samo asali.
"Muna tattauna wa da su domin ganin sun zo har Najeriya sun bawa matasan mu horo a kan wannan sabuwar fasaha kamar yadda suka yi a kasar Kamaru," a cewar Ahmad.
A cewar Ahmad, gini da kayan da aka yi daga irin sabuwar fasahar sun fi irin wadanda aka saba amfani da su kwari da nagarta.
DUBA WANNAN: Ministan Buhari ya bayyana irin mawuyacin hali da PDP ke ciki
Kazalika ya bayyana cewar suna son bawa matasa 1,000, daga manyan makarantun kasar nan, horo a kan fasahar domin su samu hanyar dogaro da kai.
Ahmed ya kara da cewa, babban kalubale da kungiyar su ke fuskanta shine yadda zata samu hadin kan gwamnati domin dorewar wannan shirin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng