El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka

El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka

Mabiya Shi'a a Najeriya karkashin kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) sunyi kira ga kasar Amurka ta sanya baki domin gwamnatin Najeriya ta saki shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky domin ya samu kulawa da lafiyarsa.

Kungiyar tayi wannan kirar ne a yau Laraba a Abuja yayin gudanar da wata zanga-zangar lumana a ofishin jakadancin Amurka. Masu zanga-zangan sunyi dirshan a gaban ofishin jakadancin dauke da hotuna masu sakonnin neman a sako El-Zakzaky.

A jawabin da ya yiwa masu zanga-zangar, sakataren kungiyar, Abdullahi Muhammad Musa ya ce kungiyar tana son Amurka ta bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya saki Sheikh Ibrahim Zakzaky daga tsaron da ake masa ba bisa ka'ida ba domin ya kula da lafiyarsa.

El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka

El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi ta'addi a harin da suka kai kauyen 'Yar Santa a Katsina

Ya kara da cewa, "Cigaba da tsare Sheikh Ibrahim Zakzaky da matarsa sai sanya 'yan kungiyar kara tsananta zanga-zangar da su keyi a Abuja musamman a harabar ofishin jakadancin na Amurka."

El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka

El-Zakzaky; Mabiya Shi'a sun garzaya ofishin jakadancin Amurka
Source: Twitter

"A matsayinku na masu asasa demokradiya, kuna ikirarin kare hakkin mutane amma an yiwa daruruwan dalibai da mata da yara kisar gilla a Zaria a 2015 amma kuna cigaba da goyon azzalumar gwamnatin Buhari.

"Akwai alamar cewa Ingila da Amurka da Isra'ila suna goyon bayan gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Yanzu ma duniya ta san cewa kisan kiyashin da akayi a Zaria shiryayen hari ne da akayi da niyyar kashe Zakzaky da kungiyarsa domin wasu kasashe su rika morar albarkatun da muke da shi."

Musa ya ce 'yan kungiyar za su cigaba da zanga-zanga a ofishin jakadancin na Amurka har sai lokacin da dauki mataki akan zaluncin da ake musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel