Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi ta'addi a harin da suka kai kauyen 'Yar Santa a Katsina

Da duminsa: 'Yan bindiga sunyi ta'addi a harin da suka kai kauyen 'Yar Santa a Katsina

- 'Yan bindiga sun kai hari kauyen Yar Santa da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina a daren jiya

- 'Yan bindigan sun tare mazaune kauyen ne a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Kankara inda suke bude musu wuta

- 'Yan bindigan sun kashe mutane hudu tare da yiwa wasu al'umma da dama munanan rauni

A daren jiya Talata 8 ga watan Janairu ne 'yan bindiga suka kai hari kauyen Yar Santa da ke karamar hukumar Kankara na jihar Katsina inda suka kashe mutane hudu tare da raunata wasu mutane da dama.

Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari a kauyen 'Yar Santa a jihar Katsina
Da duminsa: 'Yan bindiga sun kai hari a kauyen 'Yar Santa a jihar Katsina
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun kai harin ne misalin karfe 6 na yamma a yayin da yawancin mutanen garin ke hanyarsu ta komowa gida daga kasuwar Kankara inda suka tafi cin kasuwa.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da akayi a Gabon

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun iso kauyen ne a kan babura kuma suka bude wuta suna ta harbe-harbe wadda hakan yasa mutane suka rika tserewa domin su tsira da rayyukansu da dukiyoyinsu.

An nemi wasu mutane da dama ba a gansu ba bayan harin.

"Yan bindigan sun sake dawowa yau da safe yayin da muke jana'izar wadanda suka rasu sai dai 'yan banga sun fatatake su," inji shi.

A kwanakin baya, Legit.ng ta ruwaito muku cewa gwamnatin jihar ta Katsina tayi koka kan yadda 'yan bindigan suka mamaye wasu kananan hukumomi 8 a jihar.

Gwamnatin jihar ta ce akwai yiwuwar ba za ayi zabe a wadannan kananan hukumomin ba muddin ba a dauki matakin samar da tsaro ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel