Da dumi dumi: Buhari zai zabtare albashin masu daukar sama da mafi karancin albashi

Da dumi dumi: Buhari zai zabtare albashin masu daukar sama da mafi karancin albashi

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabtare albashin dukkanin wani ma'aikaci da ke daukar sama da mafi karancin albashi a kasar

- Buhari ya ce zai dukufa wajen sake fasalin ayyukan masu daukar albashi mafi karanci a kasar

- Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin shawara na shugaban kasa kan sabon albashi mafi karanci a dakin taron majalisar zartaswa na kasar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce zai zabtare albashin dukkanin wani ma'aikaci da ke daukar sama da mafi karancin albashi a kasar. A halin yanzu dai, N18,000 ne albashi mafi karanci a kasar, sai dai shugaban kasar zai mika kudurin dokar sabunta albasin zuwa N30,000, ko kuma yadda aka tsayar.

Da yake kaddamar da kwamitin shawara na shugaban kasa kan sabon albashi mafi karanci a dakin taron majalisar zartaswa a safiyar yau Laraba, ya ce zai dukufa wajen sake fasalin ayyukan masu daukar albashi mafi karanci a kasar.

Shugaban kasar, a watan da ya gabata, lokacin da yake gabatar da kasafin wannan shekarar gaban majalisar tarayya, ya ce zai kafa wani kwamiti da zai duba bukatun kwamitin shugaban kasa kan sabon albashi mafi karanci.

KARANTA WANAN: Ruguza Tinubu a Kwara: Saraki ya roki masu kada kuri'a su yafewa yan takarar PDP

Da dumi dumi: Buhari zai zabtare albashin masu daukar sama da mafi karancin albashi
Da dumi dumi: Buhari zai zabtare albashin masu daukar sama da mafi karancin albashi
Asali: Twitter

Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro, akwai mataimakin shugaban kasa, Yemi osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, da dai sauransu.

Shugaban kasar wanda ya ce an sanya sabon albashi mafi karancin a cikin kasafin kudin kasar na wannan shekarar, ya ce ya dukufa ainun wajen ganin an karawa ma'aikata mafi karancin albashi don bunkasa rayuwarsu.

"Zamu sake fasalin masu daukar albashi sama da N18,000," a cewarsa, inda ya bukace su dasu shirya da hakan.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel