Ambode ya cafke jami’in Sojan Najeriya ya bi hannun da bai dace ba

Ambode ya cafke jami’in Sojan Najeriya ya bi hannun da bai dace ba

Mun ji labari cewa gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ya taba ikin ‘yan sanda a makon nan, inda ya kama masu sabawa dokar bin hanya har kuma aka dace yayi ram da wani babban soja da laifi.

Ambode ya cafke jami’in Sojan Najeriya ya bi hannun da bai dace ba
An kama Sojan Najeriya yana tuki a sahun titin da ba na shi ba
Asali: Facebook

A Ranar Litinin dinnan ne Mai girma gwamnan jihar Legas ya bi kan titi a cikin gari inda ya rika damke masu karya doka bayan ya dawo daga garin Abuja. Gwamna Akinwumi Ambode ya kama har da wani babban Soja da laifi.

Mai girma gwamnan jihar Legas. Mista Akinwunmi Ambode yayi ram da wannan jami’in soja ne yana bin hanyar da ba ta dace ba, watau sojan ya na tuki a kan hannun da ba na sa ba, wanda hakan haramun ne a dokar hanya.

KU KARANTA: Buhari yayi tsokaci kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a Gabon

Wannan abu ya faru ne a cikin garin Ikeja inda nan ne babban birnin jihar Legas. Tuni dai gwamnan ya saka aka yi ram da motar sojar wata mai lambar JJJ 290 AC. Ana saba doka ne saboda a gujewa yawon motocin da ke kan titi.

Gwamnan yace sojan bai kamata ya saba doka a matsayin sa na jami’in tsaro wanda ya san ka’idar titi ba. Bayan nan kuma gwamnan ya kuma kama wani mutumi mai karamar mota lambar LSR 445 ER da irin wannan laifi.

Gwamnan dai ya bada umarni a karbe motocin, sannan kuma a hukunta wadanda aka samu da laifi. Ambode yayi wannan kame ne bayan ya dawo daga wani taron yakin neman zaben APC da aka yi a Abuja.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng