Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Borno, tsohon Sanata sun koma APC daga PDP

Da duminsa: Tsohon gwamnan jihar Borno, tsohon Sanata sun koma APC daga PDP

Wani tsohon gwamnan jihar Borno, Mohammed Goni ya sauya sheka daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), zuwa All Progressives Congress (APC). Goni ya kasance gwamnan tsohuwar jihar Borno daga jihar 1979 zuwa 1983.

Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya sanar da hakan ne yayinda ya jagoranci wata tawagar mutane daga yankin Arewa maso gabas zuwa wajen shugaba Muhammadu Buhari.

Yayinda yake jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa, Mr Goni ya ce ya sauya sheka zuwa APC ne saboda girman da yake baiwa shugaba Buhari da kuma irin zaman lafiyan da ya dawo yankin Arewa maso gabas.

"Na san shugaban kasan sosai, na kasance sakatare yayinda yake gwamnan Arewa maso gabas. Ma'aikaci ne".

Mr Goni ya kasance tsohon dan takaran kujeran mataimakin shugaban kasa karkashin jam'iyyar United Nigeria Peoples Party, (UNPP) kuma yayi takaran gwamnan jihar PDP a shekarar 2011.

A former senator and former speaker of old Gongola state, and a chieftain of the PDP from Adamawa state, Paul Wampana, also announced his defection to the APC.

Bugu da kari, wai tsohon sanata kuma jigon PDP. Paul Wampana, ya alanta sauya shekarsa zuwa jam'iyyar APC. Ya kasance mataimakin shugaban PDP na kasa, shiyar arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel