Rundunar Sojojin Gabon sun yi wa Shugaba Ali Bango juyin mulki

Rundunar Sojojin Gabon sun yi wa Shugaba Ali Bango juyin mulki

- Sojojin kasar Gabon sun kifar da Gwamnati mai-ci a yau dinnan

- Shugaban kasa Ali Bongo ya dade yana jinya a kasar Larabawa

- Sojoji sun ce za su dawo da mulkin farar hula a kasar ta Gabon

Rundunar Sojojin Gabon na yunkurin yi wa Shugaba Ali Bango juyin mulki

An yi wa Bango juyin mulki bayan shekaru kusan 10 a mulki
Source: Facebook

Yanzu nan mu ke samun labari daga jaridun waje cewa sojoji a kasar Gabon sun kifar da gwamnatin kasar. Rundunar sojin kasar sun mamaye gidan rediyon da ke Gabon inda su ke ta sukar halin da shugaban kasa Ali Bango yake ciki.

Wasu Dakarun Soji a Gabon sun shiga babban gidan rediyon da ake da shi a kasar inda su ka tabbatar da kifar da gwamnati mai-ci. Manema labarai sun tabbatar da cewa an ji harbe-harben bindigogi a babban birnin Libreville dazu da sassafe.

KU KARANTA: An yi tir da yadda ‘Yan Sanda su ka damke Sanatan Najeriya

Sojojin kasar na Gabon sun sanar da cewa za su kafa shugabanci na rikon kwarya inda za a nada wata majalisa ta musamman da za ta ja ragamar kasar. Sojojin sun ce za su dawo da mulkin farar hula ne bayan hambarar da gwamnatin Bongo.

Yanzu haka Ali Bongo yana kasar Morocco inda yake fama da rashin lafiya tun shekarar bara. A farkon shekarar nan ne shugaban kasar mai shekaru 59 ya aikowa mutanen kasar Gabon sako tun bayan da ya fadi da lalurar rashin lafiya a bara.

KU KARANTA: Jihar kudancin Najeriya za ta kashe fiye da Naira Biliyan 850 a 2019

Laftana Kelly Ondo Obiang, wanda shi ne shugaban dakarun da su ka karbe mulkin kasar Gabon ya bayyana cewa sakon da shugaba Bango ya aiko a makon jiya ya tabbatar da cewa shugaban bai da isasshen lafiyan cigaba da yin mulki.

A cikin makon da ya gabata ne dama shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya aiko sojoji na musamman zuwa kasar Gabon domin su kare mutanen kasar sa ko da rikici zai barke a cikin kasar ta Gabon mai dinbin arzikin man fetur.

An hambarar da Gwamnatin gidan shugaba Ali Bongo ne bayan kusan shekaru 50 su na mulkin kasar ta Afrika. Ali Bongo ya hau mulki ne a 2009 bayan Mahaifin sa Omar Bango ya mulki kasar na tsawon shekaru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel