Sojoji sun yi azamar karbe Garin Baga daga hannun ‘Yan Boko Haram

Sojoji sun yi azamar karbe Garin Baga daga hannun ‘Yan Boko Haram

Mun samu labari daga jaridar nan ta Daily Trust cewa Sojojin Najeriya su na kokarin karbe Garin Baga da wasu manyan Garuruwa akalla 5 daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno a halin yanzu.

Sojoji sun yi azamar karbe Garin Baga daga hannun ‘Yan Boko Haram
Rundunar Sojin Najeriya su na kokarin karbo Garuruwan Borno
Asali: Twitter

Yanzu da mu ke magana, bangaren Abu Mus’ab Albarnawi na Boko Haram sun ci galaba kan sojojin Najeriya a wasu Garuruwan Borno. Wadannan Gauruwa sun hada da; Baga, Doron-Baga, Kross Kawwa, Bunduran, Kekeno da Garin Kukawa.

Kwanaki ‘yan ta’addan su ka fatattaki Rundunar Sojoji daga yankin, wanda wannan ya sa Sojojin kasar su ka fara wani shiri na musamman domin ganin bayan ‘yan ta’addan. Wani babban jami’in sojan kasar ya kyankyasawa ‘yan jarida wannan.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun ji wuya a hannun sojojin Najeriya a Zamfara

Yanzu za a shirya runduna ta sojin sama da na kasa har da sojojin ruwa domin ganin an fatattaki ‘yan ta’adda daga yankin na Baga da kewaye. Sojojin za kuma su tanadi manyan makamai domin ganin sun yi wa ‘yan Boko Haram din zuwa daya.

Mutanen da ke cikin Borni sun tabbatar da cewa sun hangi Dakarun Najeriya da manyan makamai su na shiga yankin domin ganin bayan ‘yan ta’addan. Sojojin sun yi gayya ne domin ganin bayan ‘yan Boko Haram da ke fake a cikin Arewacin Borno.

Kwanan nan ne dai sojojin kasar su ka kashe sama da ‘yan ta’addan Boko Haram 200 a cikin Garin Monguno. Hakan na zuwa ne bayan ‘yan ta’addan sun kai wasu munanan hare-hare a Metele da sauran su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel