Harin Buni Gari: An sake tsinto gawar sojoji 3 cikin dokar Daji a Yobe

Harin Buni Gari: An sake tsinto gawar sojoji 3 cikin dokar Daji a Yobe

Wata majiyar rahoto kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito ta bayyana cewa, an sake tsinto gawar wasu sojoji biyu cikin dokar Daji bayan harin da ya auku kan sansanin dakarun soji da ke yankin Buni Gari a jihar Yobe.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a daren ranar Asabar din da ta gabata ne masu tayar da kayar baya na ta'addanci Boko Haram suka zartar da wani mummunan hari kan sansanin dakarun soji da ke yankin Buni Gari na jihar Yobe a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Majiyar yayin zayyanawa manema labarai rahoto a daren jiya na Alhamis ta bayyana cewa, kawowa yanzu akwai wani adadi na dakarun soji da aka nema aka rasa tun bayan aukuwar wannan mummanar ta'ada da ta bayyana a matsayin tashin hankali na kololuwa.

Harin Buni Gari: An sake tsinto gawar sojoji 3 cikin dokar Daji a Yobe

Harin Buni Gari: An sake tsinto gawar sojoji 3 cikin dokar Daji a Yobe
Source: Twitter

Wata majiyar rahoton daban ta tabbatar da cewa, an garzaya da gawar sojin biyu zuwa dakin killace gawarwaki na babban Asibitin Damaturu inda gawarwakin soji shida ke kwance gabannin sabuwar tsintuwar da halin yanzu adadin su ya kai takwas kenan.

KARANTA KUMA: Ta'addanci ya salwantar da rayukan Mutane 5,113 cikin watanni 11 a bara

Cikin rashin sa'a da kuma ban mamaki kawowa yanzu, ba bu wani rahoto da ya fito daga bangaren hukumar sojin, sai dai mun samu cewa, Kwamandan soji mai kula da atisayen Operation Lafiya Dole, Birgediya Janar Muhammad Baba Dala, a jiya Alhamis ya ziyarci Buni Gari domin ganewa idanun sa girman asarar da 'yan ta'adda suka gadar akan dakarun sa.

A wani rahoton kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, bayan kwanaki takwas da yiwa gidan Sanata shiyyar Kwara ta Yamma, Dino Melaye, ya mika wuyan sa ga jami'an tsaro na 'yan sanda kamar yadda kafar watsa labarai ta BBC ta bayyana.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel