Babu hadin-kai tsakanin hukumomin tsaro a Katsina – Gwamna Masari

Babu hadin-kai tsakanin hukumomin tsaro a Katsina – Gwamna Masari

- Gwamnatin Jihar Katsina ta na kokarin kawo karshen matsalar tsaro

- Gwamna Aminu B. Masari ya nada wani kwamiti da zai duba lamarin

Babu hadin-kai tsakanin hukumomin tsaro a Katsina – Gwamna Masari
Gwamna Masari yana kokarin kawo karshen matsalar tsaro a Katsina
Asali: Twitter

Mun samu labari cewa Gwamnatin jihar Katsina ta gano cewa akwai rashin hadin-kai tsakanin hukumomin Najeriya wajen kokarin kawo karshen satar Bayin Allah da ake yi da kuma ta’adi dabam-dabam a yankin kasar.

Bayan wani babban taro da aka gudanar a Katsina a game da sha’anin tsaro da yake cigaba da tabarbarewa, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ta gano kadan daga cikin matsalolin da ake samu, tare da shirin kawo gyara.

Sakataren gwamnatin Katsina, Dr Mustapha Inuwa, ya fadawa manema labarai cewa gwamna Aminu Bello Masari zai gana da sauran takwarorin sa gwamnonin Arewa domin ganin an shawo karshen matsalar rashin tsaron.

KU KARANTA: Dakarun Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram

Dr. Inuwa yace mai girma Rt. Hon. Aminu Masari zai zauna da gwamnan jihar Zamfara da kuma gwamnan jihar Kaduna. Haka-zalika kuma gwamnan jihar zai gana har da gwamnan jihar Maradi da ke cikin kasar Jamhuriyyar Nijar.

Gwamnatin Katsina ta kuma sha alwashin hada-kai da jami’an tsaro wajen gyara motocin ‘yan sanda da su ka lalace a jihar. Haka kuma za a maida dajin da ake garkuwa da mutane zuwa gonaki domin a rage satar jama’an.

Gwamna Masari ne dai ya nada wani kwamiti karkashin sakataren gwamnatin jihar wanda zai zauna da malamai da masu unguwa da sauran jama’a domin ganin an samu zaman lafiya a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel