Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki

- Postinor 2 magani ne da ake amfani dashi don hana shigar ciki

- Yakan hana shigar ciki idan aka sha shi a cikin kwanaki uku da yin jima'i

- Yana da illoli ga jikin mutum

Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki
Illoli da alfanun shan maganin takaita haihuwa da kiyayyar daukar ciki
Asali: Depositphotos

Postinor 2 magani ne da ke hana daukar ciki idan maniyyi ya shiga kwan halittar mace. Ko da gangan ko ba da gangan ba. Yana hana daukar ciki a kashi 95 a cikin 100 in aka sha shi a cikin sa'o'i ashirin hudu zuwa 72 bayan yin jima'i.

Amfaninsa dai shine kare kai daga daukar ciki da ba'a shiryawa ba, ko na masoya ko na ma'aurata, sai dai mutane basu san illa da zai iya kawo musu a jikinsu ba, sun fi kokarin kawai su kare daukar ciki.

Ana amfani da shi ne a matsayin matakin hana daukar ciki na gaggawa.

Anyi Postinor 2 ne yayi aiki yanda sinadarin progesterone na jikin mace ke aiki.

Ana shan postinor 2 ne a cikin kwanaki da basu kai uku bayan yin jima'i don hana daukar ciki.

Kadan daga cikin illolin Postinor 2 sune:

1. Idan aka sha shi a tsakiyar kwanakin da mace ke nasa kwan halitta, yakan hana samuwar kwan.

2. Maganin na iya canza yanayin al'adar mace. Yakan kuma canza yanayin zubar jinin, ko ya karu ko kuma ya ragu.

3. Yakan iya sanya tasowar amai wanda hakan na faruwa a kashi 25 na masu amfani da shi har su kai ga amai.

DUBA WANNAN: Ko N500 daya babu a jikin Alex Badeh sanda ya rasu, iyalansa sun karyata 'yansanda

4. Yakan iya sanya zubar jini na kwanaki biyu zuwa uku bayan shan kwayar maganin.

5. Yakan sa ciwon kai,jiri da gajiya.

6. Yakan sanya illoli da yawa idan mai amfani da kwayar na da ciwon asthma, zuciya, hawan jini, ciwon siga ko ciwon koda.

Ba a son amfani da shi a kai a kai.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel