'Yan bindiga sun kai farmaki a Kaduna, sun halaka mutum 4

'Yan bindiga sun kai farmaki a Kaduna, sun halaka mutum 4

'Yan bindiga sun kai farmaki a wasu garuruwa biyu a jihar Laduna a daren Lahadi inda suka kashe mutane hudu.

Sun kuma raunana mutane takwas sannan suka yi awon gaba da mutane biyu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sun kai harin na farko ne a Kutura Station da ke gundumar Tantatu da ke karamar hukumar Kajuru inda suka kashe mutane hudu kuma suka jikkata wasu hudu.

Harin na biyu kuma a garin Gwagwada ne da ke karamar hukumar Chikun a daren Lahadi inda aka ce an sace mutane biyu.

'Yan bindiga sun kai farmaki a Kaduna, sun kashe mutum 4

'Yan bindiga sun kai farmaki a Kaduna, sun kashe mutum 4
Source: Twitter

Wata majiya ta ce mutane takwas da aka jikkata a Kutura suna jinya a wani asibiti da ba bayyana sunansa ba.

DUBA WANNAN: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da na hannun damar Ganduje daga mukaminsa

An ruwaito cewa 'yan bindigan sun kai hari ne a garin Katura misalin karfe 8 na dare inda suka bude wuta kan wasu matasa da ke murnar shigowa sabuwar shekarar 2019.

Babu cikaken bayani a kan harin da aka kai a Gwagwada.

Kakakin hukumar 'yan sandan na jihar Kaduna, Yakubu Sabo ya tabbatar da afkuwar harin na Katura inda ya ce an kashe mutane hudu yayin da wasu uku kuma sun samu rauni.

"A jiya Lahadi misalin karfe 2.45 na dare wasu 'yan bindiga da ba san ko su wanene ba sun kai hari a Kutura da ke kauyen Kayana a karamar hukumar Kajuru na jihar Kaduna inda suka bude wuta kan mazauna kauyen da ke bikin murnar shigowar sabuwar shekara.

"Sun kashe mutane hudu sannan sun jikkata uku. 'Yan sanda sun garzaya zuwa wurin da abin ya faru inda suka kai wadanda aka yiwa rauni asibiti kuma suka bazama neman wadanda suka kai harin," inji shi.

A yayin da ya mika ta'azziyarsa da iyalan wanda suka rasu, Kwamishinan 'ya sanda Ahma Abdurahman ya bayar da tabbacin cewa 'yan sandan za suyi duk mai yiwuwa domin kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel