Yajin aiki: Hakurin mu ya kusa karewa – ‘Dalibai sun fadawa Buhari da ASUU

Yajin aiki: Hakurin mu ya kusa karewa – ‘Dalibai sun fadawa Buhari da ASUU

Mun samu labari cewa kungiyar nan ta NANS ta ‘Daliban Najeriya ta gargadi Malaman jami’o’i cewa kura tana nema ta kai bango a game da yajin aiki da ASUU ta shiga tun a farkon Watan jiya na Nuwamba.

Yajin aiki: Hakurin mu ya kusa karewa – ‘Dalibai sun fadawa Buhari da ASUU
Idan ba a sasanta da ASUU ba za a fara bore inji kungiyar NANS
Asali: Depositphotos

Kungiyar ta NANS ta bayyana cewa wa’adin da ta bada domin ASUU ta janye yajin aiki yana nan har gobe kuma da zarar wa’adin ya kare, za a ga aiki da cikawa. NANS ta ba Malaman jami’o’in zuwa karshen Watan nan ne su koma aiki.

Wani babban jami’in kungiyar NANS, Suleiman Sarki, ya tabbatar da cewa za su fara zanga-zanga muddin wa’adin da su ka gindaya ya shude ba tare da an janye yajin aikin ba. Sarki yayi wannan jawabi ne a Ranar Lahadin nan na jiya.

‘Daliban sun ce za su yi bore daga Ranar 31 ga Watan Disamba idan har aka gaza cin ma yarjeniya tsakanin ma’aikatan jami’an na kasar da kuma gwamnati. NANS tace a baya sun zara idanu ne kurum domin su ka gudun ruwan ASUU.

KU KARANTA: An kai karar Buhari har gaban Majalisar dinkin Duniya saboda yajin ASUU

Umar Faruk Lawal, wanda yana cikin shugabannin kungiyar yace ASUU tana kokarin kare bukatun ta ne kurum. Shugaban ‘Daliban na Arewacin Najeriya ya zargi Malaman kasar da cewa babu muradun al’umma da Talakawa sam a ran su.

Wani Darektan kungiyar, Anzaku Shedrack, ya bayyana cewa za su cika tituna da manyan hanyoyin kasar domin su nuna rashin jin dadin su idan har aka ki dawowa bakin aiki a makarantun jami’o’i na Najeriya bayan wannan watan.

Kungiyar tayi kira ga gwamnati da kuma Malaman kasar da su duba maslahar al’umma da ke karatu, su cin ma matsaya. An yi zama barkatai tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU amma har yanzu shiru.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel