Kungiyar IS ta Al-Baghadadi ta kwaci yanki a Borno, ta kafa tuta

Kungiyar IS ta Al-Baghadadi ta kwaci yanki a Borno, ta kafa tuta

Rahoton da muka samu daga The Cable ta ce mayakan kungiyar Boko Haram sun kafa tutarsu a garin Baga dake jihar Borno.

Wani mazaunin garin ya shaidawa majiyar Legit.ng a yammacin Alhamis cewa 'yan ta'addan sun kwace iko a garin ne bayan fattataki sojoji a sansaninsu da ke garin.

"Bayan sun fattaki sojoji daga sansaninsu kuma sun kori mutane da dama daga gidajensu, sun kafa tutarsu a garin. Babu wanda zai karyata wannan," inji wani mazaunin garin da ya nemi a sakayya sunansa.

Wani mazaunin garin mai suna Labbo Dan-Bagga shima ya tabbatar da lamarin a wani shirin gidan rediyo da aka watsa a ranar Alhamis.

Boko Haram sun kafa tutarsu a Baga bayan sun fattaki sojoji
Boko Haram sun kafa tutarsu a Baga bayan sun fattaki sojoji
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Wata mata ta datse al'aurar makwabcinta da ya dade yana cin zarafinta

"Boko Haram sun kafa tutarsu a Baga... Mun tafi masallaci muyi sallah sai muka tarar 'yan Boko Haram sun mamaye mu," inji shi.

"Sun ce kar mu tsorata kuma mu kayi sallah tare... sun ce ba za su kashe farar hula ba kuma sun 'yan bangaren Abu-Mossad Albarnawi ne na kungiyar ISWAP. Suna sanye da kaftani mai ruwan kasa da takalman sojoji. Wasu daga cikinsu sun rufe fuskokinsu."

Wata majiyar kuma ta ce 'yan ta'addan sunyi arangama da dakarun sojin Najeriya a Doron Baga, Cross Kauwa da Kukawa a jihar Borno kuma wai 'yan ta'addan sun kwace motocin yaki masu yawa.

Sama da mutane 5000 sun rasa muhallinsu a garuruwan Baga, Kukawa, Cross Kauwa a gundumar Mairiri da ke kananan hukumomin Gundunbali da Garand a jihar Borno saboda yawaitan hare-haren da 'yan ta'addan ke kaiwa.

Baya ga koran mutane daga gidajensu, mayakan Boko Haram din sun bankawa gidajensu wuta.

Mai magana da yawun hukumar sojin Najeriya, Sani Usman ya tabbatar da harin amma bai amsa tambayoyin da The Cable tayi masa ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel