Yabon goni: Tambuwal ya jinjinawa Buhari
Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yabawa kokarin gwamnatin tarayya a kokarinta na tabbatar da tsaro a jihar da ma ragowar sassan kasar nan.
Tambuwal ya yi wannan kalami ne a jiya, Laraba, yayin karbar bakuncin shugaban rundunar sojin sama a fadar gwamnatin jihar Sokoto.
Ya nuna damuwarsa bisa karuwar aiyukan ta'addanci, musamman a kan iyakokin jihar Zamfara da jamhuriyar Nijar.
Ya ce, "amadadin al'ummar jihar Sokoto, muna yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarinsa a kawo karshen asarar rayuka da dukiyoyin jama'a.
"Kusan shekaru uku kenan muna fama da rigingimu, musamman a garuruwanmu dake kan iyakar Zamfara da suka jawo asarar rayukan jama'ar mu a kauyen Tabani da kuma kwace masu gari.
"Mun yi imanin cewar idan muka hada kai tare da yin aiki tare, zamu shawo kan lamarin," a kalaman Tambuwal.
DUBA WANNAN: Duk 'yan uwan Buhari talakawa yanzu sun biloniyas - Buba Galadima
Da take jawabi, Sadique Abubakar, shugaban rundunar sojin sama ta kasa, ya ce yana jihar ta Sokoto ne bisa umarnin shugaban kasa domin kiyasin aiyukan tsaro da gwamnati ya kamata ta sani kafin ta yanke shawarar daukan matakai na warware matsalolin tsaro a yankin.
Ya kara da cewa tuni ya ziyarci jihohin Katsina da Sokoto kuma zai wuce zuwa jihar Adamawa daga Sokoto.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng