Tsibbu: Mun daina saka dan kamfai - Matan wata jami'ar Najeriya

Tsibbu: Mun daina saka dan kamfai - Matan wata jami'ar Najeriya

Dalibai mata a jami'ar jihar Delta sun bayyana cewar sun hakura da saka karamin wando na mata (pant ko "dan kanfai" da Hausa) saboda yadda matsafa ke sace masu wannan sutura domin yin tsafin samun kudi.

Matan dake karatu a jami'ar sun ce lamarin ya yi tsamarin da har ya kai ga matsafan da ake kira Yahooo Boys na tare mata su kuma tilasta su cire dab kanfansu ta hanyar nuna masu makami.

Lamarin satar dan kamfai na mata masu shekaru 14 zuwa 35 ya kai matakin da sai da gwamnatin jihar ta tashi tsaye domin yaki da masu aikata wannan muguwar dabi'a.

Wani rahoton jaridar Punch ya bayyana cewar farashin dan kamfai na budurwa kan kai kimanin Naira dubu dari uku da hamsin (N50,000), musamman idan akwai jinin al'ada a jikinsa.

Tsibbu: Mun daina saka dan kamfai - Matan wata jami'ar Najeriya
Dan kamfai
Asali: UGC

Majiyar legit.ng ta shaida mata cewar matan dake karatu a jami'ar mai matsuguni a garin Asaba na jihar Delta sun ce hanya daya da zasu tsira daga sharrin matsafan shine su daina amfani da dan kamfai kwata-kwata.

DUBA WANNAN: Sanata Wamako ya yi yayyafin kudi ga magoya bayansa, hotuna

Wata dalibar jami'ar ta ce, "mun samu labarin cewar wadannan masu tsafi na yin amfani da kamfai na mata domin yin surkullen samun kudi. An ce da zarar sun yi tsafi da kamfan mace sai ta fara zubar da jini ba kakkautawa, wasu lokutan ma an ce har aman kudi zata ke yi kafin daga bisani ta mutu. Bayan mun fara boye dan kamfan ne sai muka samu labarin cewar suna tare mata su kwace masu dan kamfai ta hanyar nuna masu bindiga, jin wannan labari ne ya sa muka yanke shawarar daina amfani da kamfai bakidaya."

Rahotanni sun bayyana cewar ko a makon jiya sai da wasu karti biyu suka tare wata dalibar jami'ar suka kwace mata dan kamfanta ta karfin tsiya da misalin karfe 8:00 na dare a kan titin Anwai a cikin garin Asaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel