2019: Za mu kawo karshen mulkin gado da Okorocha ya kafa a Imo - Oshiomhole

2019: Za mu kawo karshen mulkin gado da Okorocha ya kafa a Imo - Oshiomhole

Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole ya ce zaben Sanata Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo a zaben 2019 zai kawo karshen mulkin kama karya da Gwamna Rochas Okorocha ya ke yi a jihar Imo.

Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne a yayin da ya hallarci kaddamar da yakin neman zaben dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a jihar Imo, Sanata Uzodinma Hope a jiya a garin Owerri babban birnin jihar Imo.

Ya ce ya zo da sakon alkhairi da al'ummar jihar Imo da suka dade suna shan wahala a karkashin mulkin gwamnan da ya mayar da gidan gwamnati na gado kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

2019: Za mu kawo karshen mulkin gado da Okorocha ya kafa a Imo - Oshiomhole
2019: Za mu kawo karshen mulkin gado da Okorocha ya kafa a Imo - Oshiomhole
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Badeh ya gana da Aisha da babban hadimin Buhari kafin a kashe shi - Rahoto

A cewarsa, "Ba mun zo yin korafi bane a kan abinda ya faru a jihar nan. Mun zo ne da sakon alkhairi ga mutanen Imo. Dukkan abinda kuka gani a jihar nan mallakin mutum daya ne da iyalensa amma kuna da ikon kawo canji da cigaba a jihar."

Oshiomhole ya kara da cewa wahalhalun da al'ummar jihar suka sha zai zama alkhairi kuma ya bukaci su yiwa Okorocha sakayya da irin abinda ya musu ta hanyar zaben Hope Uzodinma da zai kawo musu canji mai alkhairi.

A jawabinsa, Sanata Hope ya yiwa mutane jihar alkawarin cewa zamanin da ake yiwa rudar mutane a jihar zai wuce. "A yau ba zanyi bayani mai tsawo ba amma ina son in tabbatar muku da cewa gwamnatin da za ta zo a gaba na al'umma ce ba na mutum daya da iyalansa ba."

Manyan mutane da suka hallarci kaddamar da yakin neman zaben sun hada da mambobin kwamittin ayyuka na APC, dukkan 'yan takarar gwamna na yankin Kudu maso gabas, Sanata Ali Modu Sherrif, mataimakin gwaman jihar Imo, Prince Eze Madumere, Sanata Benjamin Uwajumogu da mambobin hadin gwiwa na APC a jihar Imo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164