Kafa me naci ban baki ba: Jama'ar gari sun tsere bayan 'yan Boko Haram sun kai hari

Kafa me naci ban baki ba: Jama'ar gari sun tsere bayan 'yan Boko Haram sun kai hari

Wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Gajiram, hedkwatan karamar hukumar Nganzai na jihar Borno a ranar Juma'a 21 ga watan Disambar 2018.

Wasu shaidu da suka yi magana da Channels Television sun ce maharan sun iso garin cikin manyan motocci guda hudu amma dakarun sojin gwamnatin tarayya sun taka musu birki bayan sunyi musayar wuta.

Gajiram yana yankin arewacin Borno ne inda mayakan kungiyar na Boko Haram suka tsananta kai hare-hare a cikin kwanakin nan.

Kafa me naci ban baki ba: Jama'ar gari sun tsere bayan 'yan Boko Haram sun kai hari

Kafa me naci ban baki ba: Jama'ar gari sun tsere bayan 'yan Boko Haram sun kai hari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sojoji sun dakile wata sabuwar harin da 'yan bindiga suka kai a Benue

Rahotanni sun ce dakarun sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole suna fattatakar 'yan ta'addar a duk inda su kayi arangama da su ko kuma yayin da su kayi yunkurin kawo hari.

Sai dai irin wannan yunkurin harin da 'yan ta'addar ke kawo wa ya sanya al'ummar garin sun tsere cikin daji yayin da wasu da dama suna kokarin barin garin a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Kawo yanzu babu cikakken bayanin kan cewa ko akwai wadanda suka rasu ko jikkata sakamakon harin saboda har yanzu hukumar sojin Najeriya bata fitar da sanarwa game da harin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel