Kungiyar Izala tayi rabon kafafu da hannaye ga nakasassu
Kungiyar musulunci ta Jama’at Izalat al Bid’ah WaIqamatis Sunnah, (JIBWIS) tare da hadin gwiwa da Ishk Tolaram Foundation India da ke kasar India sun tallafawa mutane 3600 da suka hannaye da kafufuwarsu da na roba.
Shugaban kungiyar na kasa, Abdullahi Bala-Lau ne ya bayar da wannan sanarwan a taron manema labarai a ranar Juma'a a Abuja inda aka mika hannayen da kafafuwan ga wadanda aka tallafawa.
Bala Lau ya ce JIBWIS ta bullo da shirin ne domin taimakawa mutanen da suka rasa wasu bangarorin jikinsu kuma ba su da kudi da za su iya sayen na robar domin su cigaba da amfani da wadannan sassan jikin.
A cewarsa, JIBWIS ta baiwa mutanen irin wannan tallafin ne domin su samu ikon tsayuwa da kansu a maimakon dogara da bara domin samun abinda za su tafiyar da rayuwarsu da shi.
DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto
Ya ce, "Mutanen ba za su iya sayen wadandan sassan jikin ba saboda a kalla hannu ko kafar na roba guda daya ya kai N300,000.
"Mun bayar da tallafin ne ga mabukata ba tare da la'akari da addini ko kabilarsu ba.
"Munyi ne saboda Allah saboda mu samu sakayya a nan duniya da gobe kiyama."
Ya yi kira ga musulmi musamman masu hannu da shuni su rika tallafawa mabukata a garuruwansu.
Ya kuma yi kira ga wadanda ke rike da mulki su rika taimakawa mabukata domin hakan babban aiki ne ga bil-adama.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Dalhati Yusuf mai shekaru 33 daga jihar Plateau ya mika godiyarsa ga JIBWIS saboda tallafin da ta basu.
Ya ce, "Sana'ar acaba nake yi a baya. Na yi hatsari ne shekaru kadan da suka gabata amma yanzu ina kyautata zaton tallafin kafar da aka bani zai taimaka min in cigaba da harkoki na kamar yadda na saba."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng