'Yan Siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu

'Yan Siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce 'yan siyasar Najeriya ba su iya demokradiyya ba.

Yakubu ya yi wannan furucin ne a wurin taron masu sarautun gargajiya na Arewa karo na 5 da aka gudanar a yau Laraba a garin Kaduna kamar yadda kamfanin dillancin labarai NAN ta ruwaito.

Taken taron shine, "Rashin tsaro a shekarar zabe".

"Yan siyasar mu ba su ita demokradiyya ba shi yasa wasu daga cikinsu ke tsalle-tsalle daga wannan jam'iyyar zuwa wata jam'iyyar," inji shi.

'Yan Siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu

'Yan Siyasar Najeriya basu iya dimokuradiyya ba sam - Farfesa Yakubu
Source: Facebook

Shugaban na INEC kuma ya ci yin zabe na kasa baki daya ya fi sauki bisa gudanar da zabe a jihar guda daya kacal.

DUBA WANNAN: Amaryar sanata Yarima da ya aura tana karama ta girma, hoto

Ya bayar da misali da zaben jihar Osun da aka gudanar a watan Satumba inda ya ce an samu cigaba a zaben ta yadda aka kai kayyakin zabe rumfunan zaben a kan lokaci.

"Yin zabe a jiha guda daya yafi wahala idan aka kwantanta da yin babban zabe a jiha guda saboda idan jiha daya ake zaben dukkan mutane za su sanya ido a kan wannan zaben," inji shi.

Yakubu ya kuma jadada cewa hukumar INEC a shirye ta ke ta gudanar da sahihiyar zabe da al'umma za su amince dashi dubba da yadda ta ke kara inganta ayyukanta domin cimma yadda sauran kasashen duniya da suka cigaba su keyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel