Kwace takara: Sanata Buruji ya yi karin haske a kan hukuncin kotu

Kwace takara: Sanata Buruji ya yi karin haske a kan hukuncin kotu

Sanata mai wakiltar jihar Ogun ta gabas a majalisar dattijai kuma dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Buruji Kashamu, ya ce kotun daukaka kara ta Ibadan bata bayyana abokin hamayyar sa, Oladipupo Adebutu, ko wani dan takara a matsayin halastacce ba.

Hakan na kunshe ne cikin wani jawabi da Austin Oniyokor, mai taimakawa Sanata Buruji a bangaren yada labarai, ya raba ga manema labarai.

Adebutu, dan takarar da uwar jam'iyyar PDP ke goyon baya, na kalubalantar zaben fitar da 'yan takara da ya samar da Sanata Buruji a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ogun.

"Muna sanar da jama'a cewar labarin da abokan hamayyar mu ke yadawa kan cewar kotu ta kwace takarar gwamna daga hannun Sanata Buruji tare da mika ta hannun Adebutu ko wani dan takara, ba gaskiya bane," a cewar jawabin.

Sanata Buruji ya shaidawa magoya bayansa cewar duk da hukuncin kotun "babu abinda ya canja."

Kwace takara: Sanata Buruji ya yi karin haske a kan hukuncin kotu
Sanata Buruji
Asali: Depositphotos

A yau, Talata, ne wata kotun daukaka kara dake zamanta a Ibadan, jihar Oyo, ta kwace takarar gwamnan jihar Ogun daga hannun Sanata Buruji Kashamu tare da rushe dukkan 'yan takarar da tsagin shugabancin jam'iyyar karkashin jagorancin Adebayo Dayo ya samar.

Wannnan hukunci na kotu ya tabbatar da 'yan takarar da tsagin Honarabul Oladipupo Adebutu ya samar a matsayin karbabbu a wurin uwar jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Kungiyar Boko Haram ta saki hotunan harin da ta kai a Maiduguri

Hukuncin kotun mai alkalai uku ya jingine hukuncin kotun tarayya dake garin Abeokuta da ya tabbatar da Sanata Kashamu a matsayin dan takarar gwamna a jihar Ogun a karkashin jam'iyyar PDP.

An sa ran wannan hukunci zai kawo karshen dukkan wata dambaruwar siyasa da jam'iyyar PDP ta fada a jihar Ogun tun bayan kammala zabukan cikin gida.

Jam'iyyar PDP ce da kanta ta ta daukaka kara bayan kotun farko da ta shigar da kara ta amince da Sanata Kashamu a matsayin dan takarar gwamnan jihar Ogun a PDP.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel