Yarinyar nan da ta tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook

Yarinyar nan da ta tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook

- Ta sanya reza ta tsaga hannunta da kalamun soyayya

- Yanzu kuma wata yake so ba ita ba

- Shi bai tsaga nasa hannun ba da sunan sonta

Yarinyar da ya tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook

Yarinyar da ya tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook
Source: Facebook

Soyayya dai aka ce gamon jini, kuma kowa rabonsa yake samu a duniya. Mun samo muku labarin yarinyar nan da ta tsaga hannunta don tsabagen soyayya, yanzu dai ya zame kuma wata yake so daban, ya barta fanko, ta kai kukanta Facebook.

Yarinyar da ya tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook

Yarinyar da ya tsaga jikinta da sunan Masoyi ta kawo kararsa Facebook
Source: Facebook

Yarinyar, wadda zamu kira Aminatu, masoyiyar Hamza, ta fara sonsa tun suna yara, so da qauna da ya kaisu ga yiwa jua alkawarin aure.

Shi dai Malam Hamza, ya samu yayi makaranta, sannan yanzu haka ya sami aiki, amma kuma ga alama ya baro Aminatu a baya, inda ya ce shi 'yar Boko zai aura, ita kuwa Aminatu, bata ko gama Junior ba a sakandare.

DUBA WANNAN: Kotun daukaka kara ta wanke manyan Alkalan kasar nan daga zargin cin hanci da gwamnatin Buhari ke musu

Aminatu dai, tana ganin kamar ya yaudare tane, ya ci amanar soyayyarta, ganin har tattoo tayi wa hannunta da sunan Hamza, inda ta rubuta 'I Love U Hamxa', shi kuwa, bai taba kona ko tsaga jikinsa ba da sunan ta, hasali ma, yace shi ba mace daya zai aura ba.

Yanzu dai Aminatu na neman shawararku, ko ta yaya zaki taya ta shawo kan wannan masoyi, wanda yake wahal da soyayyar ta?

Sai ku rubuta mata shawar a dandalin muhawarmu a Facebook, zata bi kuma zata karanta, shima Hamza yana biye.

(Wannan labari dai ba dukkansa ne gaskiya ba, mun gyara shi domin yayi dadin karatu, mun kuma sakaya sunaye da wasu bayanai da soyayyar ta kunsa don adana sirrin masoyan)

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel