Tinubu na shirin yin takarar shugaban kasa a 2023 - jigo a APC

Tinubu na shirin yin takarar shugaban kasa a 2023 - jigo a APC

- Wani fusattatan jigo a jam'iyyar APC ya ce Bola Tinubu ne ya janyo rikice-rikicen da jam'iyyar ke fama da shi a yankin Kudu maso yamma

- Dan jam'iyyar ta ya nemi a sakayya sunansa ya ce zaben fidda gwani a Legas ya janyo matsaloli masu yawa da ka iya yiwa jam'iyyar illa a babban zaben 2019

- Har yanzu dai an gaza yin sulhu a tsakanin mambobin APC na Kudu maso yamma inda wasu jiga-jigan jam'iyyar da gwamnoni suka kauracewa taron sulhun

Wani fusattatan shugaba na jam'iyyar APC a reshen jihar Legas ya yi ikirarin cewa jagoran jam'iyyar na yankin Kudu maso gabas, Bola Asiwaju Ahmed Tinubu yana shirin fitowa takarar shugabancin kasa a shekarar 2023.

Shugban na jam'iyyar APC da ya nemi a boye sunansa ya kuma ce Tinubu ne dalilin da sanya ake ta fama da rikice-rikice a jam'iyyar rehen Kudu maso yamma.

Wani jigo a APC ya yi ikirarin cewa Tinubu na shirin takarar shugabancin kasa a 2023
Wani jigo a APC ya yi ikirarin cewa Tinubu na shirin takarar shugabancin kasa a 2023
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addar Zamfara, hotunan wadanda suka mutu

Ya shaidawa This Day cewa zaben fidda gwani da aka gudanar a jihar Legas ya janyo matsaloli da dama da ka iya yiwa jam'illar babban illa a babban zaben da ke tafe a shekarar 2019.

"Abin bakin ciki ne. Karshen mulkin wani mutum ya zo. Wadanda ba su gamsu da zaben fidda gwani na Legas ba za su iya yiwa jam'iyyar illa. Abinda za su iya aikatawa zai shafi zaben gwamna da na shugaban kasa. Idan har suka zartar da abinda ke zuciyarsu tabbas Legas za ta girgiza," inji shi.

"Yanzu lokaci ne na kwato wa Legas 'yancin ta. Akwai yiwuwar Tinubu ya zabi gwamna na karshe a jihar. Tinubu yana aikata duk wadannan abubuwan ne saboda ya na son ya zama shugaban kasa a 2023. Ya nada Oshiomhole da Osinbajo a APC saboda son rai.

"Wadannan halayensa za su janyo wa jam'iyyar babban asara a jihohin Ogun, Legas, Osun, Ondo, Oyo, Imo, Zamfara, Akwa Ibom, Delta, Benue, Kwara, Bayelsa, Abia da sauran jihohi inda Tinubu ke kokarin nada yaransa a matsayin gwamnoni saboda kwadayinsa na zama shuagaban kasa a 2023 bayan ya ci amanar shugaba Buhari."

Har yanzu dai an gaza yin sulhu a wasu johohin APC musamman a yankin Kudu maso yamma duk da kwamitin sulhu mai mutum 6 da jam'iyyar ta kafa wadda ta ziyarci Ekiti a ranar 10 ga watan Disamba sannan ta isa Legas a ranar 12 ga watan Disamba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel