A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya

A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Ahmed Adamu Mua'au ya ziyarci garin Bauchi bayan ya shafe shekaru uku bai ziyarci jihar ba.

Mu'azu ya shigo Najeriya a ranar Laraba domin hallartar auren diyarsa wanda aka gudanar ranar Asabar a garin Bauchi.

Wadanda suka hallarci daurin auren sun hada da abokansa, 'yan siyasa, abokan kasuwancin sa da kuma jiga-jigan jam'iyyar PDP na jiha da kasa.

A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya
A karon farko tun bayan faduwar PDP, Adamu Mu'azu ya shigo Najeriya
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Cikaken jerin sunayen mambobin majalisar wakilai da ba za su koma majalisar ba a 2019

Ana kyautata zaton ya sauka Abuja ne na dan wasu kwanaki kafin ya karasa zuwa Bauchi domin hallartar daurin auren diyar na sa a wannan makon.

Tsohon shugaban na jam'iyyar PDP ya kwashe shekaru uku baya Najeriya tun lokacin da jam'iyyar su ta sha kaye a babban zaben shugabancin kasa na shekarar 2015.

Mu'azu da ake yiwa lakabi da 'Game Changer' wato mai canja wasa ya kasance shugaban jam'iyyar PDP na kasa a lokacin da tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya sha kaye a hannun shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC.

Wasu na ganin ya bar kasar ne saboda kayen da jam'iyyar PDP ta sha a hannun APC a lokacin da ya ke shugabancin jam'iyyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel