Sai da na biya sadakin N300, 000 kuma ba auren dole aka yi mata ba inji wanda ya auri Karamar Yarinya

Sai da na biya sadakin N300, 000 kuma ba auren dole aka yi mata ba inji wanda ya auri Karamar Yarinya

A cikin ‘yan kwanakin nan ne ake ta surutu bayan an ji labarin yadda wata karamar yarinya ta auri wani Dattijon mutum tsofai-tsofai a cikin Arewa maso tsakiyar Najeriya. Yanzu dai gaskiyar lamarin ya fito fili.

Sai da na biya sadakin N300, 000 kuma ba auren dole aka yi mata ba inji wanda ya auri Karamar Yarinya
Alhaji Yakubu Umar Mainasara da Amaryar sa wajen biki
Asali: Instagram

Gidan Jaridar VOA ta Amurka ta bi diddikin labarin wannan aure da aka yi a cikin Garin Lapai a Jihar Neja inda aka gano cewa wannan Mutumi bai kai shekarun da ake ta yadawa ba, asali dai shekarun wannan Dattijo a Duniya 61.

Bayan haka kuma Iyayen wannan yarinya da aka aurar, sun bayyana cewa shekarun ta sun haura 20, akasin abin da aka rika ji a baya. Jaridar nan ta Daily Nigerian ta rahoto cewa wannan yarinya tana da shekaru 16 ne rak da haihuwa.

Wani karin bayani da mu ka samu shi ne, wannan yarinya tayi aure har sau 2 a da, don haka auren ta da wannan Dattijo ba shi ne auren ta na farko ba. Wannan ya sa Alhaji Mainasara yace sam ba yayi wa Amaryar ta sa kallon yarinya.

KU KARANTA: Dattijo dan shekara 70 ya auri yarinya yar karamar Yarinya a Najeriya

Yakubu Umar Mainasara ya kuma bayyanawa ‘Yan jarida cewa ba auren dole aka yi wa wannan Baiwar Allah ba inda yace bai tursasa mata ta aure sa ba. Wani babban Malamin addinin Musulunci a Jihar, yace auren bai saba wata doka ba.

Yanzu dai har Hukumar da ke kare hakkin kanana yara a Najeriya ta soma binciken wannan aure da aka yi tsakanin Alhaji Yakubu Umar Mainasara ‘Dan shekara 60 da Sahibar sa mai shekaru kusan 21 inda aka biya sadakin N300, 000.

A wani bidiyo, mun ga yadda wannan Budurwa ta rika tika rawa a lokacin bikin ta da wannan Dattijo, inda shi kuma yake lika mata sababbin kudi. Dazu kuma kun ji cewa Wani Matashi 'Dan Jihar Neja mai shekaru 26 ya kammala karatun PhD a Kasar waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel