Kaiƙayi koma kan mashekiya: Wata yar ƙunar baƙin wake ta kai hari a Borno, ya ƙare akanta

Kaiƙayi koma kan mashekiya: Wata yar ƙunar baƙin wake ta kai hari a Borno, ya ƙare akanta

Rundunar Yansandan jahar Borno ta sanar da samun nasarar dakile wani yunkurin harin kunar bakin wake da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram suka tura wata karamar yarinyar ta kai a cikin garin Maiduguri.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Damian Chukwu ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 13 ga watan Disamba, cikin wata hirar wayar tarho da yayi da kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN.

KU KARANTA: Za ayi jana’izar dakarun Sojojin Najeriya 100 da mayakan Boko Haram suka halaka

A cewar kwamshina Chukwu, lamarin ya faru da misalin karfe 8:30 na daren Laraba 12 ga watan Disamba a wajen garin Maiduguri, daidai lokacin da yar kunar bakin waken tayi kokarin kutsa kai shingen bincike na Yansanda don ta afka cikin Maiduguri.

Kaiƙayi koma kan mashekiya: Wata yar ƙunar baƙin wake ta kai hari a Borno, ya ƙare akanta
Yar ƙunar baƙin wake
Asali: UGC

“Karamar yarinyar dake dauke da jigidar bamabamai a jikinta tayi kokarin ratsa shingen binciken ababen hawa na Yansanda dake kan hanyar shiga garin Maiduguri, sai dai jami’anmu sun lura da ita, inda suka bindigeta.

“Karfin bindigar yasa ta yi tsalle ta fadi a gefen hanya nesa da jama’a, daga nan ne sai bamabaman dake daure a jikinta suka tashi, inda suka yi watsa watsa da namanta, ita kadai ta mutu, babu wanda ya ji ko rauni.” Inji kwamishinan.

Daga karshe kwamishinan Yansanda Damian Chukwu ya tabbatar da cewar ba tare da bata lokaci bay a tura da kwararrun jami’an Yansanda masu kwance bamabamai zuwa inda lamarin ya faru domin su tsaftace wajen.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan kasa ta Najeriya ta kammala shirin gudanar da jana’izar dakarunta guda dari da suka ransu a hannun mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yayin wani harin kwanta bauna da yan Boko Haram suka kai musu.

A watan data gabata ne mayakan Boko Haram suka kai ma dakarun bataliya ta 157 na rundunar Sojan kasa a kauyen Matele na jahar Borno, inda suka kashe Sojoji da dama daga cikinsu har da kanana da hafsoshin Soja.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel