Kananun yara fiye da Miliyan 1.3 ba su zuwa Makaranta a Kano - Kwamishina

Kananun yara fiye da Miliyan 1.3 ba su zuwa Makaranta a Kano - Kwamishina

Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa Kwamishinan harkar ilmi da kimiyya da fasaha na rikon kwarya a Jihar Kano ya bayyana irin matsalar da Jihar ke fuskanta na rashin zuwa makarantar Boko.

Kananan yara fiye da Miliyan 1.3 ba su zuwa Makaranta a Kano - Kwamishina
Kano tana fama da matsalar rashin karatun Boko na yara
Asali: UGC

Aminu Wudil ya koka da cewa yawan Mutanen Jihar Kano ta sa ana samun karuwar wadanda ba su zuwa Makaranta a Jihar. Wudil ya bayyana wannan ne lokacin da aka yi wani taro da duk masu ruwa da tsaki a harkar ilmi a Jihar.

Babban Sakataren Ma’aikatar ilmi na Kano, Danlami Garba, shi ne ya wakilci Kwamishinan a wajen wannan taro da aka yi a Ranar Lahadin da ta gabata. Garba yace Gwamnatin Jihar dai tana kashe kudi matuka wajen harkar ilmi.

Kididdigar SUBEB ya nuna cewa akwai Makarantun Gwamnati akalla 8, 280 a Kano, sannan kuma akwai Malamai kusan 60, 000. Sai dai Kwamishinan ya tabbatar da cewa akwai yara Miliyan 1.3 da ba su zuwa Makaranta a fadin Jihar Kano.

KU KARANTA: ASUU tayi kaca-kaca da wani babba a APC ta zarge sa da kashe ilmi

Harsashen da aka yi tun a 2015 ya nuna cewa akwai akalla yara miliyan 1.3 da ba su karatun Boko illa gantali a kan titinan Jihar. Bincike dai ya tabbatar da cewa a Najeriya, yara akalla Miliyan 13 ne ba su halartar makarantun Boko.

Kafin wannan rahoto mu na da labari cewa akwai yara miliyan 20 da su samun ilmin Boko a Duniya, Daga cikin wadannan kaso na sama da yara miliyan 13 a Najeriya, kusan kashi 70% sun fito ne daga Arewacin Kasar irin Kano.

A baya dai Jihar Bauchi ce tayi zarra da Yara sama da Miliyan 1.1. Yanzu dai Jihar Kano ta karbi wannan mummunan ragama. A Jihar Katsina kuma akwai yara fiye da 700, 000 a cikin wannan sahu kamar yadda mu ka ji labari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel