Gwamnatin Najeriya za kori Malaman da ba su da rajista daga aiki a 2020
Gwamnatin Tarayya ta na kokarin gyara harkar ilmi a Najeriya. Wannan ya sa Ma’aikatar ilmin Kasar ta dauki mataki na musamman domin inganta kwarewar Malaman da ke makarantun Gwamnati a Kasar.
Labari ya zo mana daga Jairdar Daily Trust cewa Gwamnatin Najeriya za ta soma sallamar duk Malaman Makarantar da ba su da cikakken rajista da lasisi daga hannun Hukumar TRCN mai yi wa Malaman kasar rajista.
Shugaban Hukumar TRCN na Najeriya, Farfesa Josiah Olusegun Ajiboye ya bayyanawa manema labarai cewa wa’adin da Gwamnatin Tarayya ta sa domin yin rajista zai kare ne a karshen Watan Disamban shekara mai zuwa.
KU KARANTA: Mu na ba yara ilmi da kayan aiki kyauta inji Gwamnan Kaduna
Kawo yanzu dai Hukumar tayi wa Malamai sama da miliyan 2 rajista a fadin kasar nan. Sai dai da zarar an shiga 2020, duk Malamin da bai da rajista zai tattara ya bar aikin sa. Olusegun Ajiboye ya tabbatar mana da wannan.
Yanzu dai ana cigaba da wayarwa Malamai kai da su kara karatu so goge, su kuma yi rajista tare da samun lasisin koyarwa a kasar. Mafi karancin abin da ake bukata kafin a yi rajista da Hukumar TRCN ita ce shaidar NCE.
TRCN tana aiki a Jihohi 6 domin bincika wadanda su ka cancanta su koyarwa da kuma wadanda bai dace su shiga aji ba. Jihohin da ake wannan aiki sun hada da: Nasarawa, Ogun, Ebonyi, Jigawa, Cross River da kuma Bauchi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng