Babban limamin kabilar Yaruba a Sokoto ya mutu

Babban limamin kabilar Yaruba a Sokoto ya mutu

Allah ya yiwa babban limamin kabilar Yaruba a jihar Sokoto, Alhaji Imran Ibrahim Lawal, rasuwa.

Kafin mutuwar sa, Alhaji Lawal, ya kasance shugaban al'ummar musulmi 'yan kabilar Yoruba a jihar Sokoto.

A sanarwar da kungiyoyin limaman kabilar Yoruba a jihar Sokoto suka fitar a yau, Lahadi, sun ce marigayin ya mutu ne a Iwo, garinsa na haihuwa, dake jihar Osun a daren juma'a bayan ya sha fama da rashin lafiya. An yi jana'izar sa jiya, Asabar, da yamma.

Dattijon mai shekaru fiye da 70, ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki da 'ya'yan jikoki.

Babban limamin kabilar Yaruba a Sokoto ya mutu
Babban limamin kabilar Yaruba a Sokoto
Asali: Twitter

Da safiyar yau din ne jaridar Legit.ng ta sanar da ku cewar labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu daga jihar Kaduna na nuna cewa Allah ya yiwa babban dan siyasa kuma tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Ahmed Aruwa, rasuwa.

DUBA WANNAN: Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa, hotuna

Majiya daga iyalansa ta bayyana wa Legit.ng cewar Sanata Aruwa ya rasu ne da safiyar yau, Lahadi, kuma za'ayi janaizarsa a masallacin Sultan Bello misalin karfe 1:00 na rana.

Aruwa ya kasance Walin Hadejia, ya wakilci mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 da 2007 inda ya rike kujeran shugaban kwamitin sufurin jirgin sama, ayyuka da gidaje, harkokin 'yan sanda, aikin noma da kuma kasafin kudi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng