Dubban mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano, hotuna

Dubban mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano, hotuna

Al'amuran yakin neman zabe na kara daukar zafi a lungu da sakon Najeriya tun bayan cikar wa'adin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta diba domin fara gudanar da yakin zabe.

A yau, Lahadi, ne uwargidan gwamnan jihar Kano, Dakta Hafsat Umar Ganduje, ta kaddamar yakin neman zaben Buhari da Ganduje.

Dakta Hafsat ta kaddamar da taron na mata zalla a garin Kofa dake karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.

Dan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji, Abdulmumin Jibril Kofa, ne ya kasance mai masaukin baki ga taron gangamin matan na yau.

Dubban mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano, hotuna
Dubban mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano
Asali: Twitter

Mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano
Asali: Twitter

Dubban mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano, hotuna
Mata sun yi taron gangamin goyon bayan Buhari da Ganduje a Kano
Asali: Twitter

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar a yayin da zaben shekarar 2019 ke kara matsowa kuma harkokin yakin neman zabe ke kara zafi, wasu jam'iyyun Najeriya, ciki har da jam'iyyar PDP, na amfani da hotunan shugaba Buhari domin samun karbuwa a wurin jama'a.

Ko shakka babu, shugaban kasa Muhammadu Buhari na sahun gaba a farinjinin a cikin 'yan siyasar Najeriya.

Duk da wasu na ganin farinjinin shugaban kasar ya ragu idan aka kwatanta da shekarun baya, har yanzu akwai wasu jam'iyyu da ke amfani da hotunansa domin samun karbuwa a wurin masu kada kuri'a.

DUBA WANNAN: Manyan arewa sun halarci jana'izar Sanata Aruwa, hotuna

Wasu daga cikin irin wadannan 'yan takara dake hada hotunansu da Buhari, sun fita daga APC ne bayan kammala zabukan cikin gida.

Daga cikin irin wadannan 'yan takara akwai Dumo Lulu-Briggs; da yanzu yake takarar neman kujerar gwamnan jihar Ribas a jam'iyyar AP, Ifeanyi Ararume; Dan takarar kujerar gwamnan jihar Imo a karkashin jam'iyyar APGA.

Karin wasu 'yan takara dake samun tallafin kamfen daga Buhari sun hada da David Ombugadu (dan takarar neman zama gwamnan jihar Nasarawa a jam'iyyar PDP), Isa Kawu (Dan takarar neman zama gwamnan jihar Neja a karkashin jam'iyyar ADP) da wasu 'yan takara a jam'iyyu daban-daban dake neman kujerar Sanata zama mamba a majalisar wakilai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel