Addinai da malumai sunyi kane-kane cikin 'yan siyasa, haka na iya dagula lamurra

Addinai da malumai sunyi kane-kane cikin 'yan siyasa, haka na iya dagula lamurra

- Da 'yan takarar zaben 2019, da maluman addnai, komai ya kankama

- Amma kuma an fara saka bangarorin su harari juna

- Malaman addinai sun kama yan takarar su kuma basu boye ba

Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Majalisar dinkin duniya tace kusan mutum miliyan daya ne basu samun agaji a Najeriya
Asali: UGC

Komai ya kankama ta bangaren yakin neman zabe a 2019. Tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na jam'iyyar APC da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP. Amma kuma an fara sako bangarorin addinai.

Shuwagabannin addinai suma sun kama yan takarar su, ba wai a shugabancin kasa dole ba, sai a jihohi.

A watannin da suka gabata, masallatai da majami'u sun koma gurin yakin neman zabe inda yan takara ke zuwa neman albarka kuma malamai suke umartar mabiya da su zabi wani Dan takara.

Wasu malaman ma har sun kai ga tsinuwa ga mabiyan addinai da suka ki sauraron umarnin su.

DUBA WANNAN: Audugar Al'ada: Shin me matan arewa ke bukata daga al'umma da gwamnatoci?

A ranar Alhamis ne kungiyar malaman catolika ta haramtawa malamai shiga tsundum cikin siyasa har ma da shiga jam'iyyun siyasa.

Sakatare Janar na kungiyar catolika ta Najeriya, Rev. Fr. Ralph Madu, ya bada sanarwar a madadin malaman catolika nuna bacin ranshi akan abinda ya faru tsakanin Rev. Fr. Ejike Mbaka da tsohon gwamnan jihar Anambra da kuma mataimakin mai takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Mista Peter Obi.

Abin ya faru ne a 2 ga watan Disamba a filin wa'azin Fr. Mbaka akan zaben 2019 mai tunkarowa.

Mbaka yayi hasashen faduwar Atiku da Obi. A wani faifan bidiyo, ya zargi Peter Obir da rashin yi wa ma jami'ar shi aiki, ya ja mishi kunnen abinda zai iya dawowa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel