Jami'ar Ebonyi ta sallami Malamai da Ma'aikata 63 kan laifukan cin zarafi da keta haddi

Jami'ar Ebonyi ta sallami Malamai da Ma'aikata 63 kan laifukan cin zarafi da keta haddi

- Lakcarori 63 sun gamu da fushin hukumar Jami'ar jihar Ebonyi a Kudancin Najeriya

- An zartar da hukuncin fatattaka daga bakin aiki kan Lakcarori 63 da wasu Ma'aikata na Jami'ar Ebonyo

- Muguwar ta'ada ta keta hada da cin zarafin gami da amfani da takardun bogi ta janyowa Ma'aikatan Jami'ar Ebonyi salalon tsiya

Hukuncin sallama da fatattaka daga bakin aiki ya tabbata kan Lakcarori 63 da wasu Ma'aikata na jam'iar jihar Ebonyi, bisa aikata munanan laifuka da muguwar ta'ada ta amfani da takardun bogi da kuma cin zarafi da keta haddi musamman ga Dalibai Mata.

Cikin wadanda jami'ar ta sallama sun hadar da Lakcarori da suka sabawa dokar jami'ar ta barin aiki bayan wa'adin su na ajiyar aiki ya riga da cika.

Sai dai rahotanni kamar yadda jaridar Sahara Repoters ta ruwaito sun bayyana cewa, mafi akasarin Ma'aikatan da jami'ar ta sallama na amfani ne da shaidar takardun bogi na kammala makarantun Sakandire.

Jami'ar Ebonyi ta sallami Malamai da Ma'aikata 63 da laifukan cin zarafi da keta haddi
Jami'ar Ebonyi ta sallami Malamai da Ma'aikata 63 da laifukan cin zarafi da keta haddi
Asali: Depositphotos

Kazalika wasu rahotannin sun ruwaito cewa, wannan hukunci na fatattaka daga bakin aiki ya shafi kimanin Ma'aikata 300 na jami'ar, illa iyaka ma'aikata 63 kacal da hukumar jami'ar ta bayyana.

Wasu daga cikin Lakcarorin jami'ar da muguwar ta'adarsu ta cin zarafi da keta haddi ta dama ma su salalon tsiya sun hadar da; Chinedu Ogah da ke bangaren nazarin tarihi da mu'amala da kasashen ketare da kuma Dakta Egbo da ke bangaren nazarin koyar da ilimi na jami'ar.

KARANTA KUMA: Atiku da jam'iyyu 41 sun gana a garin Abuja kan shirye-shiryen Zaben 2019

Kakakin jami'ar, Patrick Itumo, shine ya bayar da shaidar wannan lamari mai kunshe da damuwa da takaici yayin ganawarsa da manema labarai, inda ya ce a halin yanzu hukumar jami'ar na ci gaba da gudanar da bincike kan wasu korafe-korafe da zargi na aikata miyagun laifuka.

A yayin haka jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Ministan Ilimi Mallam Adamu Adamu, ya bayyana cewa kaso 1 cikin 3 na al'ummar Najeriya sun tsunduma tsundum cikin duhu na Jahilci sakamakon rashin neman ilimi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel