Masu juna biyu 30 ke mutuwa a Zamfara kulli yaumin - Kungiyar Likitocin Najeriya

Masu juna biyu 30 ke mutuwa a Zamfara kulli yaumin - Kungiyar Likitocin Najeriya

- Likitoci 345 kacal jihar Zamfara ke da shi

- Babu kayayyakin aiki a asibitocin jihar, game da cewar Dr Batur

Akalla mata masu juna biyu 30 ke mutuwa kowace rana a jihar Zamfara, mataimakin shugaban kungiyar likitocin Najeriya, Dr Mannir Bature, ya laburta.

Dakta Bature ya bayyana hakan ne a taron lakca da kungiyar Advocay Nigeria ta shirya domin inganta rayuwan matada yara a jihar Zamfara. Ya alakanta mutuwan mata da yara a jihar da rashin ingantaccen kiwon lafiya a jihar

Yace: "A jihar Zamfara a yau, yawan mutane sama da miliyan hudu, likita daya ke kula da mutane 1000 sabanin bukatar kungiyar kiwon lafiyan duniya."

Ya ce jihar na da likitoci 345 a jihar gaba dayanta. Birnin Gusau mai yawan mutane 600,000 na da likitoci 275 kacal yayinda sauran kananan hukumomin 13 na raba likitoci 75.

KU KARANTA: Dan majalisa ya fice da APC

Yayinda yake magana kan kayan aiki a asibitocin jihar, Dakta Bature yace babu asibitin jihar Zamfara dake da na'urori nebulizer, oxygen, suction da na daukan hoto.

Yace: "Babu sashen kula da kananan yara a dukkan asibitocin jihar kuma an daina inganta ma'aikata ta hanyar turasu horo."

"Wasu abubuwan dake dakile cigaban kiwon lafiya a jihar shine rashin kyakkyyawan albashi ga ma'aikata da kuma rashin basu karfin guiwa."

Shi yasa duk lokacin da aka alanta neman ma'aikatan asibiti a asibitin gwamnatin tarayya, za ka ga ma'aikatan jihar Zamfara suna guduwa."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel