Kuma dai: ASUP za ta fara yajin aiki sai baba ta gani a cikin mako mai zuwa

Kuma dai: ASUP za ta fara yajin aiki sai baba ta gani a cikin mako mai zuwa

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiya da Fasaha ta Kasa (ASUP), ta ce za ta fara yajin aikin gama gari daga ranar 12 ga watan Disambar 2018.

Malaman Kwalejin Kimiyoyin suma za su hade da takwarorinsu na Jami'o'i da suka kwashe wata guda suna yajin aikin.

A hirar wayar tarho da ya yi da Premium Times a safiyar Laraba, Shugaban ASUP na kasa, Usman Dutse ya ce gwamnatin tarayya ta gaza cika wa kungiyar alkawurran da ta dauka.

Kafin fara yajin aikin, kungiyar ta bai wa gwamnati wa'addin kwanaki 21 kuma daga baya da dage har zuwa watan Nuwamba amma duk da hakan gwamnati ba ta dauki mataki ba.

Kungiyar malaman Kwalejojin Fasaha za ta shiga yajin aikin gama gari
Kungiyar malaman Kwalejojin Fasaha za ta shiga yajin aikin gama gari
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda Saraki ya ci amanar mu a kan biyan bukatar sa - Tinubu

Mr Dutse ya ce wannan yajin aikin da za su fara na gama gari ne kuma babu takamammen ranar da za su janye.

"Gwamnati ta gaza cika alkawurran da ta yiwa kungiyar kamar yadda ya ke a cikiin yarjejeniyar fahimtar juna da suka rattaba hannu a kai a Kwalejin Fasaha da ke Yaba a Legas a makon da ta gabata," inji shi.

ASUP ta tafi yajin aiki a watan Nuwamban 2017 amma gwamnati ta yi yarjejeniya da kungiyar a kancewa zata aiwatar da shawarwarin da NEEDS na shekarar 2014, haka yasa aka janye yajin aikin bayan kwanaki 15.

Yarjejeniyar ya bukaci gwamnati ta kara kudaden da ta baiwa kwalejojin kimiyyar.

Mr Dutse ya kume ce gwamnati da majalisar tarayya ba su bawa ilimi muhimmanci wajen samar da kudaden tafiyar da makarantu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164