Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke

Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke

- Kusan shekara daya kenan da ake ta yada cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu

- Hakan ta fara yaduwa ne sakamakon bidiyo da Nnamdi Kanu yayi

- Kanu ya zargi cewa Jibril Aminu daga kasar Sudan ne ke mulkin Najeriya

Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke

Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke
Source: Twitter

Labarin ya fara ne daga bakin shugaban masu son kafa kasar Biafra, da jagoransu Nnamdi Kanu. Kanu yace wani ne a Aso Rock ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kuma yayi barazanar fallasa yanda aka maida wani Jibril Adamu don maye gurbin mataccen shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar London.

Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke

Wasu dai sun zargi wai shugaba Buhari ya rasu, an zaci wasa suke ashe da gaske suke
Source: Depositphotos

Ya zargi cewa Jibril yayi kama da Buhari bambancin su kawai hanci mai fadi d hannayen yara da yake dasu.

Fasuwar labarin ke da wuya yan Najeriya da yawa har ma da manyan kasar suka yarda da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rasu amma an maye gurbin shi da mai kama dashi daga Sudan.

Kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta sun cika da labarin tare da bidiyon cewa ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne a Aso Rock ba.

DUBA WANNAN: Yadda yara suka kashe Mamman Nur na Boko Haram

Kanu ya fara yada labarin ne bayan da shugaban kasa yana ta zuwan UK sakamakon rashin lafiyar shi. Fadar shugaban kasa ta sanar cewa ciwon kunne ke damun shugaban.

Amma dadewar da yayi a wata tafiyar neman lafiya da yayi kuma ba tare da labarin komai ba game da ciwon dake damun shi yasa aka zargi cewa ciwon yayi zafi kuma ba zai iya cigaba da jagorantar mu ba.

Bayan kusan wata daya ne sai shugaban kasa ya dawo daga doguwar tafiyar shi.

Bidiyo ne da mutane sama da dubu biyar suka yada a Facebook da Twitter. A bidiyon, Kanu yake magana ga magoya bayan Buhari cewa "Mutumin da kuke gani a talabijin ba Buhari bane, Sunan shi Jibril daga Sudan."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Mailfire view pixel