Da dumi dumi: EFCC ta kama wani dan kasar waje da dala miliyan 2 a filin jirgin Abuja

Da dumi dumi: EFCC ta kama wani dan kasar waje da dala miliyan 2 a filin jirgin Abuja

Jami’an hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin azrikin kasa zagon kasa ta cafke wani mutumi dan kasar Lebanon, Abbas Lakis da wasu makudan kudade da suka kai dala miliyan biyu, kwatankwacin naira miliyan dari bakwai da arba’in kenan a filin sauka da tashin jirage na babban birnin tarayya Abuja.

Legit.com ta ruwaito jami’an EFCC sun cafke Abbas ne a filin tashin jirage na Abuja bayan samun bayanan sirri dage wasu majiyoyi daban daban na cewa yana dauke da kudade daya dauko daga jahar Kano yake kokarin fitar dasu.

KU KARANTA: Mataimakin Atiku Abubakar ya tabbatar da babu hannun Buhari a cikin matsalolin Najeriya

Da dumi dumi: EFCC ta kama wani dan kasar waje da dala miliyan 2 a filin jirgin Abuja

Abbas
Source: UGC

Da jami’an suka tareshi, suka fara gudanar da bincike akan kayansa inda suka bankado kudi $2,104, 936 da fam dubu dari da sittin da uku da dari bakwai da arba’in (£163, 740) da kuma yiro dubu dari da arba’in da hudu da dari shida da tamanin (€144, 680)

Sauran kudaden da aka gano daga hannun Abbas un hada da riyar dubu dari uku da casa’in da daya da dari takwas da talatin da takwas (R391,838) frank na kasar Swiss dubu uku da dari hudu da ashirin (CHF 3,420), dirham dubu goma da dari da talatin da biyar da kuma kudin kasar China dubu goma, da wasu kudaden wasu kasashe da dama.

Daga karshe hukumar tace zata gurfanar da Abbas gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike.

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta gurfanar wani ma’aikacin gwamnatin tarayya, Bello Na Allah Yabo, mataimakin darakta a hukumar kula da Yansandan Najeriya, a gaban kotu kan zarginsa da handamar kudi naira miliyan da dari da arba’in da biyar da dubu dari uku da arbain da biyu da sittin da uku (N145, 342, 063).

Hukumar ta bayyana cewa Yabo yayi amfani da mukaminsa na jami’I mai biyan Yansandan dake aikin a jahar Ekiti albashi a shekarar 2015, ya sace kudaden don amfanin kansa, inda ya boye kudin a asusun bankinsa na Unity.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel