Amfani da illolin rake ga Mata ma su juna biyu

Amfani da illolin rake ga Mata ma su juna biyu

Da yawan mata da ke dauke da juna biyu na yawan tambayar ko akwai wani amfani a tattare da shan rake yayin da ciki ya fara tsufa? Shin ko babu matsala mace mai juna biyu ta ke shan rake? Ko shan rake na taimakon jaririn dake ciki ko ya yi ma sa wata illa?. Amsar masana lafiya a kan wadannan tambayoyi sun kasu gida biyu; amfani da kuma illar shan rake yayin juna biyu.

Amfanin rake ga mace mai juna biyu: A yayin da mace ke da juna biyu, duk abinda ta ci ko ta sha na da tasiri ga lafiyar dan da ke cikin mahaifar ta.

Sanannen abu ne cewar yawan cin 'ya'yan itace da tasiri wajen inganta lafiyar dan da ke cikin mahaifa. Rake dan itace ne da ke da ruwa mai zaki.

Rake na dauke da sinadarin protein da ke taimakon kwayoyin halittar jikin dan adam.

Mata ma su ciki kan fuskanci taurin bahaya. A cikin ruwan rake akwai sinadaran da ke sa ka bahaya laushi, bisa wannan dalili, masana sun bayyana cewar shan rake na da kyau ga ma su juna biyu.

Amfani da illolin rake ga Mata ma su juna biyu
Amfani da illolin rake ga Mata ma su juna biyu
Asali: UGC

Ruwan rake na taimakon hanta. Hanta na daga cikin halittun jiki da ke shan wahala yayin juna biyu, a saboda haka shan rake zai taimakawa hanta.

Rake na kara karfin garkuwar jiki. Masana sun bayyana cewar shan rake yayin da ciki ya fara tsufa zai bawa mace kariya daga kamuwa daga kananan cututtuka. Sai dai, masanan sun ce shan rake a farkon shigar juna biyu kan iya lalata shi. Hakan na faruwa ne saboda karfin garkuwar jiki kan yiwa sabon juna biyu karfi.

DUBA WANNAN: Sirrikan cin ayaba ga namiji

Ruwan rake na bawa jiki kuzari. Ruwan rake, duk da zakinsa, na dauke da karancin sindarin sukari da ke tunzura ciwon sukari.

Mace mai juna biyu da ke yawan shan rake za ta yi maganin kasala da mata su juna ke yawan fuskanta.

Masana sun bawa mata ma su juna shawara a kan shan rake kamar haka:

Idan za a sha ruwan rake, to a sha da zarar an kammala matse shi, kar a bari ya dade saboda akwai sinadaran da su ke zama guba idan aka bari su ka dade bayan an matse su daga jikin karan raken.

Yana da kyau mace mai juna biyu ta fara neman shawarar likita kafin fara ci ko shan wani abu sabo.

Idan mace mai juna biyu na da ciwon sukari, ta fara neman tuntubar likita kafin ta fara shan rake don gudun kar a samu taruwar sukari a cikin jininta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel