Harin Metele: Adadin sojojin da aka kashe ya karu

Harin Metele: Adadin sojojin da aka kashe ya karu

- An gano cewa Sojoji 113 ne aka kashe a harin da Boko Haram suka kai a Metele da ke jihar Borno

-Har ila yau, akwai kuma wasu dakarun Sojoji 153 da har yanzu ba a gano inda suke ba

- A baya hukumar sojin ta ce jami'an sojoji 13 ne suka rasu a sakamamakon harin da 'yan ta'addan suka kai a ranar Lahadi

Harin Metele: Adadin sojojin da aka kashe ya karu
Harin Metele: Adadin sojojin da aka kashe ya karu
Asali: Facebook

Rahoton da Premium Times ta wallafa ya bayyana cewa a kalla sojoji 113 na 157 bataliya suka rasa ransu sakamakonn harin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a ranar 18 ga watan Nuwamba a sansanin soji da ke Metele.

An kuma tabbatar cewa har yanzu akwai wasu sojoji 153 da ba a gano inda suke ba kimanin mako guda bayan harin da aka kai a sansanin na sojin kamar yadda wasu manyan shugabanin soji suka fadi.

DUBA WANNAN: An kashe kuku bisa zarginsa da sata a gidan gwamna Dankwambo

Wadanda aka kashe sun hada da kwamandan bataliyan wanda majiyar Legit.ng ta bayyana cewa soja ne mai mukamin laftant kwanel.

An kuma gano cewa mataimakin kwamandan bataliyan da jami'in leke asiri da kuma wasu manyan jami'an soji biyu suna daga cikin wadanda aka kashe a harin da Boko Haram ta kai misalin karfe 6 na yammacin Lahadi da ta gabata.

A ranar 20 ga watan Nuwamba da Premium Times ta fara wallafa labarin harin, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa kwamandan battaliyan ne kawai ya rasu da wasu sojoji 12.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: