Asiri ya tonu: An kama wani dan majalisa yana amfani da shaidar karatu ta bogi

Asiri ya tonu: An kama wani dan majalisa yana amfani da shaidar karatu ta bogi

Babban jami’I a sashin kula da daukan dalibai a jami’ar gwamnatin tarayya dake Jos, Monday Danjem ya bayyana gaban kotu, inda ya shaida mata cewa dan majalisar dokokin jahar Filato Ibrahim Hassan na amfani ne da takardar shaidar kammala karatu na jami’ar, amma fa na bogi.

Legit.com ta ruwaito dan majalisa Ibrahim Hassan yana wakiltar mazabar Jos da Arewa ne a majalisar dokokin jahar, kuma yana shan tuhuma a gaban kotun ne daga abokin hamayyarsa da suka yi takara tare a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a 2015.

KU KARANTA: Abota ta zama kiyayya: Wani mahauci ya kashe abokinsa da duka daya a Jigawa

Wanda ya shigar da karan, Abdul Saleh ya maka Hassan gaban kotu ne kan zarginsa da yin amfani da takardar karatu ta bogi, ta difloma a ilimin tafiyar da kasuwanci da yake ikirarin ya samu ne daga jami’ar Jos bayan shafe shekaru yana karatu a cikinta.

Don haka Saleh ke tuhumar Hassan akan mika ma hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, wannan shaidan karatu na bogi, kuma a haka ya fafata a zabe a shekarar 2015, har yayi nasara a jam’iyyar APC ta baba Buhari.

Amma a zaman cigaba da sauraron karar da aka yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamba, Rajistran jami’ar Jos da kansa ya bayyana ma Alkalin babbar kotun tarayya dake sauraron karar cewa jami’ar Jos bata san Hassan ba, kuma bai taba karatu a jami’ar ba, haka zalika ba shi ya sanya hannu akan takardar da yake amfani da it aba, don haka ta bogi ce.

Wannan dai shine karo na biyu da Mista Danjem ke bayyana kotu gaskiyar abinda ya sani game da ingancin takardar shaidar karatun da Hassan ke amfani da ita, inda a watan Disambar data gabata ma sai da ya aika ma kotun da takardun dake nuna Hassan bai yi karatu a jami’ar Jos ba.

Danjem ya tabbatar ma kotu cewa ranar da Hassan ke ikirarin ya samu shaidar kammala karatun difloma dake rubuce akan takardar tasa, watau 25 ga watan Nuwambar 1996 basu yaye dalibi ko daya ba. daga karshe Alkali Kurya ya dage sauraron karar zuwa ranar 29 da 30 ga watan Nuwamba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel