Farashin kayayyaki sun sauko a kasuwannin kayan masarufi a Najeriya

Farashin kayayyaki sun sauko a kasuwannin kayan masarufi a Najeriya

- An ruwaito cewa hauhawan kaya ya sauka daga kashi 11.28 zuwa 11.26

- Tsadar kayan ya karu ne da kashi 0.74 a watan Octoba daga kashi 0.09 na watan Satumba

- Jimillar kuma shine kashi 12.78 daga kashi 13.16 cikin dari

Farashin kayayyaki sun sauko a kasuwannin kayan masarufi a Najeriya
Farashin kayayyaki sun sauko a kasuwannin kayan masarufi a Najeriya
Asali: Depositphotos

NBS ta ruwaito cewa a kididdigar ta, hauhawar kaya ta sauka daga kashi 11.28 zuwa 11.26 a cikin dari.

Sakamakon binciken farashin kayan abinci ne da hauhawar su a Najeriya wanda ake yi wata wata. An samu karuwar kashi 0.74 a watan Octoba wanda hakan ya nuna raguwa ne da kashi 0.09 daga kididdigar watan Satumba.

Rahoton ya na cewa "Jimillar kididdigar na watannin 12 da suka gabata na shine kashi 12.78 daga 13.16."

DUBA WANNAN: An zabo wata mace a matsayin mataimakiyar shugaban kasa a tikitin ANN

Rahoton ya nuna cewa akwai jihohi ne a kasar nan ke fuskantar saukar farashin daga watan Satumba zuwa Octoba na wannan shekarar. Jihohin sun hada da jihar Kogi, Filato da Nasarawa, Akwa Ibom, Benue, Kwara da Ondo.

A watan Octoba rahoton ya nuna cewa akwai jihohin da suke fuskantar hauhawan farashin kayan abinci, sun hada da Bayelsa, Abuja, Taraba, Bauchi, Oyo da jihar Filato.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel