Gyaran ilimi: Gwamna Masari zai sama matasa 2000 aikin koyarwa a Katsina

Gyaran ilimi: Gwamna Masari zai sama matasa 2000 aikin koyarwa a Katsina

Gwamnatin jahar Katsina ta kammala shirin daukan sabbin Malaman sakandari guda biyu dake da kwarewa a fannoni daban daban don koyarwa a makarantun sakandarin jahar Katsina, inji rahoton jaridar daily trust.

Majiyar Legit.com ta ruwaito sakataren gwamnatin jahar Katsina, Mustapha Muhammad Inuwa ne ya sanar da haka a ranar Talata yayin da yake rangadin cibiyoyin da ake gudanar da aikin biyan albashin malaman firamari su dubu biyar dake karkashin tsarin S-Power.

KU KARANTA; Harin ta’addanci: An kashe mutane 50 a yayin bikin maulidi

Inuwa ya bayyana cewa suma Malaman sakandarin da ake sa ran dauka aiki zasu kasance a karkashin tsarin aikin S-Power ne, wani shirin tallafa ma matasa marasa aikin yi da gwamnatin jahar Katsina ta bullo da shi kwatankwacin N-Power.

Cikin sanarwar da Inuwa ya fitar ta bakin daraktan watsa labaru na ofishin sakataren gwamnatin jahar Katsina Abubakar Aliyu Yar’adua ya bayyana cewa a yan kwanakin da suka gabata ne gwamnati ta samar da naira miliyan 400 don biyan bashin albashin Malaman S-Power na watanni hudu.

Sakataren ya bada uzurin wannan tsaiko da aka samu wajen biyan albashin, inda yace wasu matsaloli ne da suka danganci tsare tsaren aiki da na kashe kudi suka taso, amma daga yace sun shawo kan matsalar, kuma daga yanzu tare da ma’aikatan gwamnati za’a dinga biyansu albashinsu na N20,000 kowani wata.

Sai dai sakataren yayi kira ga malaman da su rama ma gwamnati aniyarta, ta hanyar dagewa wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata, domin kuwa daga cikinsu gwamnati zata zakulo masu hazaka don maye duk wani gurbi da aka samu a aikin koyarwa na dindindin a jahar.

Daga karshe kuma yayi kira dasu tabbata sun sanar da hukumar dake kula da S-Power a duk lokacin da suka samu aikin da yafi wannan kuma suka tafi, don daukan matakin daya dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng